Ku riskar da (kason gado) ta hanyar farillai ga ma'abotansu, abin da ya rage to namiji ma…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Ku riskar da (kason gado) ta hanyar farillai ga ma'abotansu, abin da ya rage to namiji ma…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Ku riskar da (kason gado) ta hanyar farillai ga ma'abo…
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «أَلْحِقُوا الفَرَائِضَ بِأَهْلِهَا، فَمَا بَقِيَ فَلِأَوْلَى رَجُلٍ ذَكَرٍ».
Bayanin hadisin: Ku riskar da (kason gado) ta hanyar farillai ga ma'abo…
Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- ya umarci masu raba gado da su raba wa waɗanda suka cancanci rabon bisa adalci kamar yadda sharia ta yi bayani, kamar yadda Allah Yake nufi, sai a baiwa magada abin da Allah ya kaddarawa kowa a cikin Littafinsa, shi ne biyu cikin uku, da ɗaya cikin uku, da ɗaya cikin shida, da Rabi, da ɗaya cikin huɗu, da ɗaya cikin takwas. Abin da ya yi saura bayan wannan, to sai a baiwa mafi kusanci ga mamacin daga cikin maza; su ake kira Asubai.
Koyarwar hadisin: Ku riskar da (kason gado) ta hanyar farillai ga ma'abo…
- Hadisin ƙa'ida ce a cikin rabon gado (dukiyar da mamaci ya bari).
- raba gado yana farawa ne ta hanyar farawa da masu ci da lamba .
- Abin da ya rage bayan ci da farilla to sai abaiwa asibai.
- Gabatar da mafi kusanci sannan mafi kusanci, dan haka asibi ba ya gado kamar baffa tare da samun asibin da ya fi shi kusanci kamar uba.
- Babu komai ga asibi idan ci da lamba ya ƙarar da dukkanin dukiyar da mamaci ya mutu ya bari, wato bai bar komai ba daga cikinsu.
Rukunan :
RABON GADO
· MASU CINYE SAURA
· FIƘHU DA USULU
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الله أكبر
Allah Shi ne Mafi Girma