Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana buɗe sallah…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana buɗe sallah…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare…

Bayanin hadisin: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare…

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta yi bayanin sallar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana buɗe sallarsa da kabbarara harama, sai ya ce: «Allahu Akbar (Allah ne Mafi girma)», kuma yana buɗe karatu da Suratul Fatiha: «Alhamdu lillahi rabbil aalamin (Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai)...». Ya kasance idan ya yi ruku'u bayan tsayuwa, ba ya ɗaga kansa sama kuma ba ya sunkuyar da shi a lokacin ruku'u, kawai yana maida shi daidai wa daida, idan ya ɗago kansa daga ruku'u sai ya tsayu a tsaye kafin ya yi sujjada, idan ya ɗaga kansa daga sujjada ta farko, ba ya sujjada ta biyu har sai ya tabbata a tsaye. Ya kasance yana zama bayan kowanne raka'o’i biyu dan yin tahiya kuma yana cewa: «Attahiyyatu lillahi was salawat waɗɗaibat(Gaishe-gaishe sun tabbata ga Allah da salloli da tsarkakan ayyuka)...», kuma ya kasance idan ya zauna tsakanin sujjadu biyu ko dan tahiya sai ya shimfiɗa ƙafarsa ta hagu ya zauna a kanta, ya kuma kafa ƙafarsa ta dama. Kuma yana hana mai sallah a cikin sallarsa ya zauna kamar zaman shaiɗan, hakan shi ne ya shimfiɗa ƙafafuwansa akan ƙasa, kuma ya zauna akan ƙarshensu, ko ya ɗanfara mazaunansa a ƙasa ya kafa ƙwaurukansa ya kuma ɗora hannayensa akan ƙasa kamar yadda kare yake yi, ko mai sallah ya shimfiɗa zira'insa ya shimfiɗasu a cikin sujjada kamar yadda namun daji suke yi . Kuma ya kasance yana cika sallarsa da yin sallama: «Assalamu alaikun warahmatullah» daga dama sau ɗaya, ɗayan kuma daga hagu.

Koyarwar hadisin: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · SIFFAR SALLAH · KURAKUREN MASU SALLAH

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah