Wanda ya tsarkake Allah a bayan kowacce sallah sau talatin da uku, kuma ya gode wa Allah s…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Wanda ya tsarkake Allah a bayan kowacce sallah sau talatin da uku, kuma ya gode wa Allah s…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Wanda ya tsarkake Allah a bayan kowacce sallah sau tala…

Bayanin hadisin: Wanda ya tsarkake Allah a bayan kowacce sallah sau tala…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya ce bayan ƙare sallar farilla:

Sau talatin da uku: "Tsarki ya tabbata ga Allah" (Subhanallah) shi ne tsarkake Allah daga tawaya.

Da kuma talatin da uku: "Godiya ta tabbata ga Allah" (Alhamdulillah) shi ne yabo gareShi da siffofin cika tare da sonSa da girmamaShi.

Da talatin da uku: "Allah ne Mafi girma" (Allahu Akbar) shi ne cewa Allah ne Mafi girma kuma Mafi ɗaukaka daga dukkan komai.

Da cike adadin ɗarin da faɗin: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake, ba shi da abonkin tarayya, kuma Shi mai iko ne a kan dukkan komai. Ma’anarsa: Babu abin bauta da cancanta sai Allah Shi kaɗai, ba shi da abonkin tarayya, kuma Shi Maɗaukakin Ya keɓanta da cikakken mulki, wanda ya cancanta da Yabo da kambamawa tare da so da girmamawa banda wanda ba shi ba, kuma Shi mai iko ne babu abin da yake gagarar sa.

Wanda ya faɗi hakan an shafe masa kurakuransa kuma an gafarta masa su, ko da sun kasance kwatankwacin farar kunfa ce wacce take saman kogi lokacin da ya kwaranyo.

Koyarwar hadisin: Wanda ya tsarkake Allah a bayan kowacce sallah sau tala…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · ZIKIRAN SALLAH

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah