Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ɗaga han…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ɗaga han…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a…
عَن ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَرْفَعُ يَدَيْهِ حَذْوَ مَنْكِبَيْهِ إِذَا افْتَتَحَ الصَّلَاةَ، وَإِذَا كَبَّرَ لِلرُّكُوعِ، وَإِذَا رَفَعَ رَأْسَهُ مِنَ الرُّكُوعِ، رَفَعَهُمَا كَذَلِكَ أَيْضًا، وَقَالَ: «سَمِعَ اللَّهُ لِمَنْ حَمِدَهُ، رَبَّنَا وَلَكَ الحَمْدُ»، وَكَانَ لاَ يَفْعَلُ ذَلِكَ فِي السُّجُودِ.
Bayanin hadisin: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kasance yana ɗaga hannayensa agurare uku a sallah, daura da kafaɗa wanda shi ne: Matattarar ƙashin kafaɗa da damtse.
Guri na farko: Idan zai buɗe sallah yayin kabbarar harama.
Na biyu: Idan Zai yi kabbara dan ruku'u.
Na uku: Idan ya ɗago kansa daga ruku'u kuma ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareka.
Ya kasance ba ya ɗaga hannayensa a lokacin fara sujjada, ko lokacin ɗagowa daga sujjada.
Koyarwar hadisin: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a…
- Daga hikimomin ɗaga hannaye a cikin sallah cewa hakan ado ne ga sallah da kuma girmama Allah - tsarki ya tabbatar maSa -.
- Ɗaga hannaye ya tabbata daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - aguri na huɗu a cikin riwayar Abu Humaid al-Sa'idi a wajen Abu Dawud da waninsa, shi ne lokacin tasowa daga tahiyar farko a sallah mai raka'a uku da mai raka'a huɗu.
- Ya tabbata daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi yana ɗaga hannayensa daura da kunnuwansa ba tare da shafa ba, kamar yadda yake a cikin riwayar Malik ɗan Huwairis a cikin Bukhari da Muslim: "Cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi kabbara yana ɗaga hannayensa har sai ya zo dasu daura da kunnuwansa".
- Haɗawa tsakanin Tasmi'i da Tahmidi wannan ya keɓanci liman da mai sallah shi kaɗai ne kawai, amma mamu sai ya ce: Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareKa.
- Faɗin: "Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareKa" bayan ruku'u ne kamar yadda ya inganta daga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinsa akwai sigogi huɗu, wannan ɗaya ce daga cikinsu, abin da yafi nutum ya bibiyi wadannan sigogin ya zo da wannan wani lokaci, wani lokacin kuma da wannan.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· SALLAH
· FIƘHU DA USULU
· SIFFAR SALLAH
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا إله إلا الله
Babu abin bautawa sai Allah