Koma ka yi sallah domin cewa kai baka yi sallah ba

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Koma ka yi sallah domin cewa kai baka yi sallah ba

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Koma ka yi sallah domin cewa kai baka yi sallah ba

Bayanin hadisin: Koma ka yi sallah domin cewa kai baka yi sallah ba

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga masallaci, sai wani mutum ya shigo a bayansa sai ya yi sallah raka'a biyu da gaggawa, bai nutsu a cikin tsayuwarsa da ruku'unsa da sujjadarsa ba, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana lura da shi a cikin sallarsa, sai ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a lokacin Ma’aikin Allah yana zaune a gefen masallaci sai ya yi masa sallama, sai ya amsa masa sallamar, kuma ya ce masa: Ka koma ka sake sallarka, domin kai baka yi sallah ba. Sai ya dawo yana sallah da gaggawa kamar yadda ya yi sallar, sannan ya zo sai ya yi sallama ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce masa: Ka koma ka yi sallah; domin kai baka yi sallah ba, ya aikata haka sau uku. Sai mutumin ya ce: Na rantse da wanda Ya aikoka da gaskiya, ba zan iya yin wacce tafi wannan ba to ka koya mini, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Idan ka tashi zuwa sallah to ka yi kabbarar harama, sannan ka karanta Fatiha da kuma abinda Allah Ya so ka karanta, sannan ka yi ruku'u har sai ka natsu kana mai ruku'u, shi ne ka sanya tafukanka biyu akan gwiwoyinka sai ka miƙar da bayanka ka tabbata dan yin ruku'inka, sannan ka ɗago ka daidaita bayanka har sai ƙasusuwa sun koma mararrabarsu kuma ka daidaita a tsaye, sannan ka yi sujjada har sai ka natsu kana mai sujjada, shi ne ka tabbatar da goshi tare da hanci, da hannaye da gwiwoyi da geffan diga-digai akan ƙasa, sannan ka ɗago har sai ka natsu kana zaune tsakanin sujjada biyu, sannan ka aikata hakan a kowace raka'a ta sallarka.

Koyarwar hadisin: Koma ka yi sallah domin cewa kai baka yi sallah ba

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · SIFFAR SALLAH

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
سبحان الله وبحمده Tsarkin Allah da godiyarSa

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah