Wanka ranar Juma'a wajibi ne akan kowanne baligi, kuma ya yi asuwaki, ya shafa tirare in…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Wanka ranar Juma'a wajibi ne akan kowanne baligi, kuma ya yi asuwaki, ya shafa tirare in…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Wanka ranar Juma'a wajibi ne akan kowanne baligi, kum…
Bayanin hadisin: Wanka ranar Juma'a wajibi ne akan kowanne baligi, kum…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanka ranar Juma'a abu ne mai karfi kamar wajibi a hakkin kowanne namiji baligi daga musulmai daga wanda juma'a ta wajaba akansa, kuma ya tsaftace hakoransa da asuwaki da makancinsa, ya kuma shafa tirare da kowanne irin tirare mai kanshi.
Koyarwar hadisin: Wanka ranar Juma'a wajibi ne akan kowanne baligi, kum…
- Karfafar mustahabbancin wanka ranar Juma'a akan kowanne mutum musulmi baligi.
- Tsafta da kawar da wari mara kyau abin nema ne a shari'a ga kowanne musulmi.
- Girmama ranar Juma'a, da yin tanadi saboda ita.
- Karfafa mustahabbancin asuwaki a Juma'a.
- Anso Shafa tirare da kowanne irin tirare mai ƙanshi kafin tafiya Juma'a.
- Mace idan ta fita daga gidanta dan sallah ko waninta, to tirare ba ya halatta gareta; Dan nunin sunna akan haramcin hakan.
- Wanda ya isa mafarki shi ne baligi, balaga tana faruwa ne da wasu alamomi. Uku daga ciki mace da namiji suna tarayya a cikinsu, su ne: Na farko: Cikar shekara goma sha biyar. Na biyu: Idan gashi mai kauri ya tsiro a gefen farji. Na uku: Zubar maniyyi ta hanyar mafarki ko ta hanyar sha'awa koda ba tare da mafarki ba. Amma alama ta hudu to ita ce take kebantar mace, ita ce kuwa: Al’ada, idan mace ta yi al’ada to ta zama baliga.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· SALLAH
· FIƘHU DA USULU
· SALLAR JUMA'A
· HUKUNCE-HUKUNCEN SALLAR JUMA'A
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الحمد لله
Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah