Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Wanda ya yi wanka irin wankan janaba a ranar Juma`a, sannan ya tafi, kamar ya bayar da sad…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da falalar gaggawar tafiya zuwa sallar Juma'a. Gaggawa tana farawa ne daga bullowar rana zuwa lokacin zuwan liman; shi ne sa'o'i biyar, ana karkasasu kaso biyar gwargwadan lokaci tsakanin bullowar rana har zuwa shigowar liman da hawansa minbari dan huɗuba:
Na farko: Wanda ya yi wanka cikakke kamar wankan janaba, sannan ya tafi masallacin Juma'a a lokaci na farko kamar ya yi sadaka da taguwa ne.
Na biyu: Wanda ya tafi a lokaci na biyu kamar ya yi sadaka da saniya ne.
Na uku; Wanda ya tafi a lokaci na uku kamar ya yi sadaka ne da rago - shi ne namijin tinkiya - mai ƙahuhhuna.
Na huɗu: Wanda ya tafi a lokaci na huɗu kamar ya yi sadaka ne da kaza.
Na biyar: Wanda ya tafi a lokaci na biyar kamar ya yi sadaka ne da ƙwai.
Idan liman ya fito dan huɗuba; sai mala'ikun da suke zaune a ƙofofi dan rubuta masu shiga masallaci na farko da mai biye da shi sai su dakatar da rubutu, sai su zo suna jin zikiri da huɗuba.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · TSARKI · SALLAH · FIƘHU DA USULU · WANKA · SUNNONI DA LADUBBAN WANKA · SALLAR JUMA'A