Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Manzon Allah -tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya kasance- yana yin hudub…
Ingantacce ne duka Riwayoyin nasa guda biyunTeburin Abun ciki :
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن عبد الله بن عُمر بن الخطاب رضي الله عنهما قال: «كان النبي صلى الله عليه وسلم يخطب خطبتين يقعد بينهما» وفي رواية لجابر - رضي الله عنه-: «كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يَخْطُبُ خُطْبَتَيْنِ وهو قائم، يفصل بينهما بجلوس».
Ranar juma`a matattara ce babba gamammiya ga mutanen gari baki dayan su saboda haka ne annabi tsira da aminci sukara tabbata a gareshi ya kasance daga cikin hikimar sa yana yiwa mutane huduba ranar juma`a hudubobi guda biyu, yana fuskantar da su izuwa dukkan alherai a cikin hudubobin guda biyu, yana tsawatar da su ga barin sharri ya kasance yana zuwa da hudubobi guda biyu alhali yana tsaye akan munbari, don ya kasance ya kai isa matuka cikin koyar da su da yimusu wa`azi, da abinda ke ciki na tsayuwa wajen bayyanar da karfin musulunci da bashi cikakkiyar kulawa. idan ya gama da hudubar farko, sai ya zauna zama sassauka don ya dan huta, sai ya raba tsakanin ta farko da ta biyu, sa`annan ya mike yayi huduba ta biyu saboda kada mai huduba ya gaji mai sauraro kuma ya kosa.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · SALLAR JUMA'A