Na shiga ni da Mahaifina ga Abu Baraza Al-aslami, sai Mahaifina ya ce da shi:yaya Annabi S…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Na shiga ni da Mahaifina ga Abu Baraza Al-aslami, sai Mahaifina ya ce da shi:yaya Annabi S…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Na shiga ni da Mahaifina ga Abu Baraza Al-aslami, sai M…

عن أبي المنهال سيار بن سلامة قال: (دَخَلتُ أنا وأبي علَى أبي بَرزَة الأسلمي، فقال له أبي: كيف كان النبي صلى الله عليه وسلم يصلي المَكْتُوبَة؟ فقال: كان يُصَلِّي الهَجِير -التي تدعونها الأولى- حِينَ تَدحَضُ الشَّمسُ. ويُصَلِّي العَصرَ ثم يَرجِعُ أَحَدُنَا إلى رَحلِه في أَقصَى المدينة والشَّمسُ حَيَّة، ونَسِيتُ ما قال في المَغرب. وكان يَسْتَحِبُّ أن يُؤَخِّر من العِشَاء التي تَدعُونَها العَتَمَة، وكان يَكرَه النَّوم قَبلَهَا، والحديث بَعدَها. وكان يَنْفَتِلُ من صَلَاة الغَدَاة حِين يَعرِفُ الرَّجُل جَلِيسَه، وكان يَقرَأ بِالسِتِّين إلى المائة).

Bayanin hadisin: Na shiga ni da Mahaifina ga Abu Baraza Al-aslami, sai M…

Abu Barzah -Allah ya yarda da shi- ya fadi lokutan Sallar Farilla, Sai ya fara da cewa shi Annabi SAW ya Kasance yana Sallar Azahar, lokacin da Rana ta Karkata daga daga tsakiyar Sama zuwa Yamma, kuma wannan shi ne farkon lokacinta, kuma yana Sallar La'asar, sannan daya daga Masallatan ya dawo gidan sa a mafi nisan wuri daga Madina kuma Rana bata gushe ba tana nan, wannan shi ne farkon lokacinta, amma Magriba Mai riwayar ya manta abunda ya zo cikinta, kuma Nassoshi sun nuna haka Ijma'in Malamai kan cewa farkon lokacin ta da faduwar Rana, kuma Manzon Allah ya Kasance yana son ya jinkirta Isha, Saboda lokacinta wanda ya fi shi ne a Sallaceta a karshen lokacinta Na Mukhtari, kuma ya Kasance yana kin ayi Bacci kafinta don tsoron ya jinkirta ta daga lokacinta Mukhtari ko ya rasa Jam'i, da kuma tsoron bacci ya cimmasa da kuma barin Sallar dare kuma yana kin yin Hira bayanta saboda tsoron makara ga barin Sallar Asuba, ko rasa Sallar jam'i, Kamar yadda yana tafiya bayan Sallar Asuba, a lokacin da Mutum yana iya gane waye yake zaune a gefensa, tare da cewa zai Karanta a cikin sallarsa Aya Sittin zuwa dari, daga cikin abunda ya ke nuna cewa shi yana Sallatarta da duku duku.

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · SHARUƊAN SALLAH

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah