Azaba ta wuta ta tabbata ga karshen kafa ku cika alwala
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Azaba ta wuta ta tabbata ga karshen kafa ku cika alwala
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Azaba ta wuta ta tabbata ga karshen kafa ku cika alwala
Bayanin hadisin: Azaba ta wuta ta tabbata ga karshen kafa ku cika alwala
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi tafiya daga Makka zuwa Madina a tare da shi akwai sahabbansa, sai suka samu ruwa a hanyarsu, sai wasu daga sahabbai suka yi gaggawar alwala dan sallar La'asar har karshen kafafuwansu suka dinga bayyana ga mai kallo saboda bushewarsu daga ruwa, sai Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Azaba da halaka a cikin Wuta sun tabbata ga masu takaitawa a wanke karshen kafa a lokacin alwala, kuma ya umarcesu da sukai matuka a cikin cika alwala.
Koyarwar hadisin: Azaba ta wuta ta tabbata ga karshen kafa ku cika alwala
- Wajabcin wanke kafafuwa a alwala; domin da shafa ya halatta da wanda ya bar wanke karshen kafa ba'a yi masa narko da wuta ba.
- Wajabcin game dukkan gabban da ake wankewa da wankewa da ruwa, kuma wanda ya bar wani sashi karami daga abinda ya wajaba a wanke shi da gangan da kuma sakaci to sallarsa ba ta inganta ba.
- Muhimmancin ilimantar da jahili da kuma shiryar da shi.
- Malami ya yi inkarin abinda yake gani na tozartar da farillai da sunnoni ta hanyar da ta dace.
- Muhammad Ishak al-Dahlawi ya ce: Cika (alwala) nau'i uku ne: Farilla shi ne game gaba da (ruwa) sau ɗaya, da sunna shi ne wankewa sau uku, da kuma mustahabbi shi ne tsawaitawa tare da wankewa sau uku.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· TSARKI
· FIƘHU DA USULU
· ALWALA
· SIFFAR ALWALA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا حول ولا قوة إلا بالله
Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah