Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjad…
Hasan ne a baki dayan Riwayoyin saAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن ابن عباس رضي الله عنهما: كان النبي صلى الله عليه وسلم يقول بين السجدتين: «اللَّهمَّ اغْفِرْ لي، وارْحَمْنِي، وعافِني، واهْدِني، وارزقْنِي».
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance yana yin Addu’a tsakanin sujjada biyu a Sallarsa, da waɗannan addu’o’in biyar, wacce Musulmi yake da matuƙar buƙatar su, kuma sun ƙunshi alheran duniya da lahira, kamar neman gafara, da ɓoye zunubi, da kuma yafe su, da malalo rahama da waraka daga shubuhohi da abubuwan sha’awe-sha’awe da rashin lafiya da cututtuka , da kuma roƙon Allah samun shiriya a kan gaskiya da kuma tabbata a kanta, da arziki na imani da ilimi da aiki na ƙwarai da kuma dukiya ta halal mai daɗi.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · SIFFAR SALLAH · ZIKIRAN SALLAH