ya ku mutane, kawai na aikata haka ne don ku yi koyi da ni, kuma ku san sallata

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > ya ku mutane, kawai na aikata haka ne don ku yi koyi da ni, kuma ku san sallata

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: ya ku mutane, kawai na aikata haka ne don ku yi koyi da…

عن أَبِي حَازِمِ بْن دِينَارٍ: أَنَّ رِجَالًا أَتَوْا سَهْلَ بْنَ سَعْدٍ السَّاعِدِيَّ، وَقَدِ امْتَرَوْا فِي الْمِنْبَرِ مِمَّ عُودُهُ، فَسَأَلُوهُ عَنْ ذَلِكَ، فَقَالَ: وَاللهِ إِنِّي لَأَعْرِفُ مِمَّا هُوَ، وَلَقَدْ رَأَيْتُهُ أَوَّلَ يَوْمٍ وُضِعَ، وَأَوَّلَ يَوْمٍ جَلَسَ عَلَيْهِ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، أَرْسَلَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِلَى فُلَانَةَ -امْرَأَةٍ من الأنصار قَدْ سَمَّاهَا سَهْلٌ-: «مُرِي غُلَامَكِ النَّجَّارَ أَنْ يَعْمَلَ لِي أَعْوَادًا أَجْلِسُ عَلَيْهِنَّ إِذَا كَلَّمْتُ النَّاسَ»، فَأَمَرَتْهُ فَعَمِلَهَا مِنْ طَرْفَاءِ الْغَابَةِ، ثُمَّ جَاءَ بِهَا، فَأَرْسَلَتْ إِلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَمَرَ بِهَا فَوُضِعَتْ هَاهُنَا، ثُمَّ رَأَيْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ صَلَّى عَلَيْهَا وَكَبَّرَ وَهُوَ عَلَيْهَا، ثُمَّ رَكَعَ وَهُوَ عَلَيْهَا، ثُمَّ نَزَلَ الْقَهْقَرَى، فَسَجَدَ فِي أَصْلِ الْمِنْبَرِ ثُمَّ عَادَ، فَلَمَّا فَرَغَ أَقْبَلَ عَلَى النَّاسِ فَقَالَ: «أَيُّهَا النَّاسُ، إِنَّمَا صَنَعْتُ هَذَا لِتَأْتَمُّوا وَلِتَعَلَّمُوا صَلَاتِي».

Bayanin hadisin: ya ku mutane, kawai na aikata haka ne don ku yi koyi da…

Wasu mutane sun zo wa ɗaya daga sahabbai suna tambayarsa game da minbarin Annabi wanda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya riƙeshi: Da me aka yi shi? Haƙiƙa sun yi jayayya a hakan, sai ya ambata musu cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aika zuwa ga wata mata daga Mutanen Madina tana da wani yaro kafinta, sai ya ce da ita: Ki umarci yaronki ya yi min minbarin da zan zauna a kansa lokacin da zan yi wa mutane magana, sai matar ta amsa, ta umarci yaronta ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - minbari na bishiyar Ɗarfa'u, lokacin da ya gama sai matar ta aika da munbarin zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya yi umarni da shi sai aka ajiye shi a wurinsa a masallaci, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi sallah a kansa ya yi kabbara alhali yana kansa, sannan ya yi ruku'u alhali yana kansa, sannan ya sauka yana tafiya ta baya, ba tare da ya juyo da fuskarsa ba zuwa ta baya ba, sai ya yi sujjada a asalin minbarin sannan ya dawo, lokacin da ya gama sallar sai ya fuskanci mutane, ya ce: ya ku mutane, kaɗai na aikata haka ne don ku yi koyi kuma ku san sallata.

Koyarwar hadisin: ya ku mutane, kawai na aikata haka ne don ku yi koyi da…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · SIFFAR SALLAH

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah