na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai ni ne mafi kusancinku kamanceceniya da sal…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai ni ne mafi kusancinku kamanceceniya da sal…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai ni ne m…

عن أَبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه: أنه كَانَ يُكَبِّرُ فِي كُلِّ صَلَاةٍ مِنَ الْمَكْتُوبَةِ وَغَيْرِهَا، فِي رَمَضَانَ وَغَيْرِهِ، فَيُكَبِّرُ حِينَ يَقُومُ، ثُمَّ يُكَبِّرُ حِينَ يَرْكَعُ، ثُمَّ يَقُولُ: سَمِعَ اللهُ لِمَنْ حَمِدَهُ، ثُمَّ يَقُولُ: رَبَّنَا وَلَكَ الْحَمْدُ، قَبْلَ أَنْ يَسْجُدَ، ثُمَّ يَقُولُ: اللهُ أَكْبَرُ حِينَ يَهْوِي سَاجِدًا، ثُمَّ يُكَبِّرُ حِينَ يَرْفَعُ رَأْسَهُ مِنَ السُّجُودِ، ثُمَّ يُكَبِّرُ حِينَ يَسْجُدُ، ثُمَّ يُكَبِّرُ حِينَ يَرْفَعُ رَأْسَهُ مِنَ السُّجُودِ، ثُمَّ يُكَبِّرُ حِينَ يَقُومُ مِنَ الْجُلُوسِ فِي الِاثْنَتَيْنِ، وَيَفْعَلُ ذَلِكَ فِي كُلِّ رَكْعَةٍ، حَتَّى يَفْرُغَ مِنَ الصَّلَاةِ، ثُمَّ يَقُولُ حِينَ يَنْصَرِفُ: وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ، إِنِّي لَأَقْرَبُكُمْ شَبَهًا بِصَلَاةِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، إِنْ كَانَتْ هَذِهِ لَصَلَاتَهُ حَتَّى فَارَقَ الدُّنْيَا.

Bayanin hadisin: na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai ni ne m…

Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - yana ruwaito wani yanki daga siffar sallar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, yana ba da labarin cewa ya kasance idan ya tashi yin sallah yana kabbarar harama a yayin da yake miƙewa, sannan ya yi kabbara a yayin da yake cirata zuwa ruku'u, da yayin da yake yin sujjada, da yayin da yake ɗago kansa daga sujjada, da yayin da yake yin sujjada ta biyu, da yayin da yake ɗago kansa daga gareta, da yayin da yake miƙewa daga raka'a biyun farko bayan zama don tahiyar farko a sallah mai raka'a uku ko huɗu, sannan ya aikata hakan a dukkanin sallah har sai ya gamata, ya kasance yana cewa a yayin da ya ɗago bayansa daga ruku'u: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, sannan ya ce alhalin yana tsaye: Ya Ubangijimmu godiya ta tabbata a gareKa.

Sannan Abu Huraira yake cewa a yayin da ya idar da sallar: Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, lallai ni ne mafi kusancinku kamaceceniya da sallar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan ita ce siffar sallarsa har ya bar duniya.

Koyarwar hadisin: na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai ni ne m…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · SIFFAR SALLAH

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
سبحان الله وبحمده Tsarkin Allah da godiyarSa

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah