Wanda ya sallaci irin sallarmu kuma ya fuskanci alƙiblarmu, kuma ya ci yankanmu to wannan …
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Wanda ya sallaci irin sallarmu kuma ya fuskanci alƙiblarmu, kuma ya ci yankanmu to wannan …
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Wanda ya sallaci irin sallarmu kuma ya fuskanci alƙibla…
Bayanin hadisin: Wanda ya sallaci irin sallarmu kuma ya fuskanci alƙibla…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya lazimci shari'un addini na zahiri cewa ya yi irin sallarmu, kuma ya fuskanci alƙiblarmu, kuma ya ci yankanmu yana mai halatta shi ; to wannan shine musulmin da yake da amanar Allah da ManzonSa da kuma alƙawarinSa, dan haka kada ku warware amanar Allah da alƙawarinSa a cikinsa.
Koyarwar hadisin: Wanda ya sallaci irin sallarmu kuma ya fuskanci alƙibla…
- Ibnu Rajab ya ce: Wannan hadisin ya yi nuni akan cewa jini ba ya zama abin tsarewa da mujarradin shahada biyu, har sai ya tsaya da haƙƙoƙinsu, kuma mafi ƙarfin haƙƙoƙinsu ita ce sallah; saboda haka ne ta keɓanceta da ambato, a cikin wani hadisin daban ya raɓa zakka zuwa ga sallah.
- Al'amarin mutane abin ɗauka ne akan zahiri banda baɗini, wanda ya bayyanar da alamomin addini za'a gudanar da hukunce-hukuncen Musulmai a kansa muddin dai bai gudanar da saɓanin hakan ba.
- Ibnu Rajab ya ce: Ambatan fuskantar alƙibla nuni ne zuwa cewa babu makawa da zuwa da sallar musulmai wacce aka shara'anta a cikin littafinsu wanda aka saukar ga annabinsu ita ce sallah da fuskantar Ka'aba, inba haka bafa wanda ya yi sallah zuwa Baitul Maƙdisi bayan anshafeta kamar Yahudawa ko kallan gabas kamar Nasara to ba musulmi ba ne, koda ya yi shaidar tauhidi.
- A cikinsa akwai dalili akan girman gurin fuskantar alƙibla a sallah, domin cewa a cikin sharuɗɗan sallah bai ambaci waninta ba, kamar tsarki da waninsa.
- Ibnu Rajab ya ce: Amabatansa cin yankan musulmai a cikinsa akwai nuni zuwa cewa babu makawa daga lazimtar dukkanin shari'un musulunci na zahiri, kuma mafi girmansu shine cin yankan musulmai, da kuma dacewa da su a cikin yankansu, duk wanda ya hanu daga hakan to ba musulmi ba ne.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· ABIBCICCIKA DA ABUBUWAN SHA
· SALLAH
· Rulings of Animals Slaughtered by the Disbelievers
· ILIMIN AƘIDA
· FIƘHU DA USULU
· WAJIBCIN SALLAH DA HUKUNCIN MAI BARINTA
· SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE
· MUSULUNCI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا حول ولا قوة إلا بالله
Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah