Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wanka, ko ya kasanc…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wanka, ko ya kasanc…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -…
Bayanin hadisin: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wankan janaba da sa'i zuwa mudu biyar, kuma yana alwala da mudu. Sa'i: Mudu haɗu, mudu kuma: Gwargwadan cikin tafuka biyu na mutum madaidaicin halitta.
Koyarwar hadisin: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -…
- Halaccin tattali a ruwan alwala da wanka, da rashin ɓarna, koda ruwan ya kasance mai sauƙin samu ne.
- An so ƙaranta ruwan alwala da wanka gwargwadan buƙata, kuma wannan shi ne shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Abin nufi cikawa a alwala da wanka tare da kula da sunnoni da ladubba ba tare da ɓarna ko ƙwauro ba, kuma a kiyaye lokaci da yawan ruwan da ƙarancinsa da wanin hakan.
- Ana anbaton janaba ga dukkan wanda ya zubar da maniyyi ko ya yi jima'i, kuma an anbaceta da hakan dan mai ita yana nisantar sallah da ibadu har sai ya tsarkaka daga gareta.
- Sa'i: wani abin awo ne sananne, abin nufi da shi sa'in Annabi, awonsa yakai nauyi (480) na alkama mai kyau, a lita kuma (lita 3).
- Mudu: Awone na shari'a, shi cikin tafuka biyu ne na mutum madaidaici idan ya cikasu ya miƙe hannunsa da su. Mudu shi ne ɗaya bisa huɗu na sa'i da haɗuwar masana fiƙihu, gwargwadansa ML (750).
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· TSARKI
· FIƘHU DA USULU
· ALWALA
· SUNNONI DA LADUBBAN ALWALA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
اللهم صل على محمد
Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad