Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Babu wani musulmin da zai yi alwala ya kyautata alwalarsa, sannan ya tashi ya yi sallah ra…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1Annabi - tsira da amincin Alah su tabbata agare shi - ya yi bayani alhali shi yana zantar da mutane falala biyu masu girma:
Na farko: Wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwalar ya cikata ta fuskar da aka sunnanta, kuma ya ba kowace gaɓa haƙƙinta na ruwa, sannan ya ce: Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad bawan Allah ne kuma ManzonSa ne; sai an buɗe masa ƙofofin aljanna takwas zai shiga ta wacce yake so.
Na biyu: Wanda ya yi wannan alwalar cikakkiya, sannan ya tashi bayan alwalar ya yi sallah raka'a biyu; yana mai fuskantosu da zuciyarsa da ikhlasi da ƙanƙar da kai, ya ƙanƙar dakai da fuskarsa da dukkan gaɓɓan jikinsa saboda Allah, sai aljanna ta wajaba gare shi.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · TSARKI · FIƘHU DA USULU · ALWALA · SUNNONI DA LADUBBAN ALWALA