Mun kasance ba ma daukar kalar hanta-hanta da fatsi-fatsi a bakin komai bayan tsarki
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Mun kasance ba ma daukar kalar hanta-hanta da fatsi-fatsi a bakin komai bayan tsarki
Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud ne ya ruwaito shi da wannan lafazin, kuma Bukhari ya ruwaito shi ba tare da ƙarin (bayan tsarki) ba
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Mun kasance ba ma daukar kalar hanta-hanta da fatsi-fat…
Bayanin hadisin: Mun kasance ba ma daukar kalar hanta-hanta da fatsi-fat…
Sahabiyya Ummu Adiyya - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa mata a zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba sa daukar ruwan da yake fita daga farji - wanda launinsa yake karkata zuwa baƙi, ko fatsi-fatsi - bayan ganin tsarki cewa yana daga al’ada, saboda haka ba sa barin sallah ko azimi saboda shi.
Koyarwar hadisin: Mun kasance ba ma daukar kalar hanta-hanta da fatsi-fat…
- Ruwan da yake zuba daga farjin mace - bayan tsarkaka daga al’ada - ba'a izina da shi koda a tare da shi akwai launin hanta-hanta da fatsi-fatsi wanda ya samu ta hanyar jini.
- Zubar hanta-hanta da fatsi-fatsi a lokacin al’ada da al'ada ana daukarsa a matsayin al’ada; Domin cewa shi jini ne a lokacinsa, sai dai mai cakuduwa ne da ruwa.
- Mace ba ta barin sallah ko azimi saboda hanta-hanta da fatsi-fatsi wanda yake a bayan tsarki, kawai ta yi alwala ta yi sallah.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· TSARKI
· FIƘHU DA USULU
· HAILA DA BIƘI DA ISTIHALA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
اللهم صل على محمد
Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad