Ki zauna gwargwadan abinda hailarki take riƙe ki, sannan ki yi wanka
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Ki zauna gwargwadan abinda hailarki take riƙe ki, sannan ki yi wanka
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Ki zauna gwargwadan abinda hailarki take riƙe ki, sanna…
عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضي الله عنها أَنَّهَا قَالَتْ: إِنَّ أُمَّ حَبِيبَةَ بِنْتَ جَحْشٍ الَّتِي كَانَتْ تَحْتَ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ عَوْفٍ شَكَتْ إِلَى رَسُولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم الدَّمَ، فَقَالَ لَهَا: «امْكُثِي قَدْرَ مَا كَانَتْ تَحْبِسُكِ حَيْضَتُكِ، ثُمَّ اغْتَسِلِي». فَكَانَتْ تَغْتَسِلُ عِنْدَ كُلِّ صَلَاةٍ.
Bayanin hadisin: Ki zauna gwargwadan abinda hailarki take riƙe ki, sanna…
Daya daga cikin sahabbai mata ta kawo koken zubar jini (jinin Istihara) zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da take fama da shi, sai ya umarceta ta dakatar da sallah gwargwadan abinda hailarta take tsareta kafin zuubar wannan al'amarin da ya faru da ita, sannan ta yi wanka ta yi sallah, ta kasance tana wanka dan neman lada a kowacce sallah.
Koyarwar hadisin: Ki zauna gwargwadan abinda hailarki take riƙe ki, sanna…
- Jinin cuta (Wato jinin istihala) shi ne: Fitar jini ya zarce ga mace bayan kwanukan hailarta data saba.
- Mai jinin cuta tana daukar kanta mai haila gwargwadan kwanukan da haila taka zo mata a cikinsu, kafin abinda ya sameta ya sameta na jinin cuta.
- Idan gwargwadan kwanukan al'adarta na asali suka shude, to ita ana daukarta mai tsarki daga al’ada - koda cewa jinin cuta yana tare da ita - sai ta yi wankan daukewar jinin al’ada.
- Mai jinin cuta wanka ba ya wajaba akanta a kowacce sallah; domin wankanta - Allah Ya yarda da ita - ya kasance da ijtihadi ne daga gareta, da a ce ya kasance wajibi ne da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana mata shi.
- Alwala tana wajaba akan Mai jinin cuta a kowacce sallah; domin hadasinta madawwami ne ba mai yankewa ba ne, misalinta dukkan wanda karinsa madawwami ne kamar wanda a tare da shi akwai yoyon fitsari, ko fitar tusa mai a koyaushe.
- Tambayar ma'abota ilimi daga abinda yake rikitarwa a al'amuran Addini, yayin da wannan matar ta kawo kuka ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta tambaye shi game da yawan jinin da yake samunta.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· TSARKI
· FIƘHU DA USULU
· HAILA DA BIƘI DA ISTIHALA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
حسبنا الله ونعم الوكيل
Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye