Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Wannan dinnan jijiya ce, saidai ki bar sallah a gwargwadan kwanukan da kika kasance kina …
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1Fadima 'yar Hubaishin ta tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Lallai ni jini ba ya yanke mini, yana zarcewa har a lokacin da ba na al’ada ba, shin hukuncin hakan zai zama hukuncin al’ada sai inbar sallah? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mata: Lallai shi jinin cuta ne, shi jinin rashin lafiya ne yana faruwa daga yankewar jijiya a mahaifa, ba jinin haila ba ne, Idan lokacin haila ya zo wanda kika kasance kina haila a cikinsa akan al'adarki ta wata kafin ki yi rashin lafiya da jinin cuta, to ki bar sallah da azimi da wasunsu , na abinda haila take hanawa a lokacin al’ada . Idan gwargwadan lokacin ya kare sai ki zama kin yi tsrki, to sai ki wanke gurin jinin, sannan ki wanke jikinki cikakken wankewa dan dauke hadasi, sannan ki yi sallah.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · TSARKI · FIƘHU DA USULU · HAILA DA BIƘI DA ISTIHALA