Na kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya kai zuwa …

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Na kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya kai zuwa …

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Na kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su t…

عَنْ حُذَيْفَةَ رضي الله عنه قَالَ: كُنْتُ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَانْتَهَى إِلَى سُبَاطَةِ قَوْمٍ، فَبَالَ قَائِمًا، فَتَنَحَّيْتُ فَقَالَ: «ادْنُهْ» فَدَنَوْتُ حَتَّى قُمْتُ عِنْدَ عَقِبَيْهِ فَتَوَضَّأَ فَمَسَحَ عَلَى خُفَّيْهِ.

Bayanin hadisin: Na kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su t…

Huzaifa Dan Yaman - Allah Ya yarda da su - yana bada labarin cewa shi ya kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya so ya yi fitsari, sai ya shiga jujin wasu mutane; shi ne gurin da ake zubar da tsummokara da sharar da ake sharewa a cikin gidaje, sai ya yi fitsari alhali shi yana tsaye, ya kasance mafi yawancin al'adarsa shi ne ya yi fitsari a zaune.

Sai Huzaifa ya yi nesa da shi, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce masa: Ka kusanto, sai Huzaifa ya kusanto gare shi har ya tsaya a bayansa daura da ƙarshen diga-digansa; dan ya zama kamar kariya gare shi daga kallonsa a wannan halin.

Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi alwala, lokacin wanke ƙafafuwansa biyu, sai ya wadatu da shafa akan kuffinsa biyu - su ne abinda ake ɗaurawa a ƙafa na fata mara kauri da makamancinta kuma yana zama mai suturce idan sawu - kuma bai ciresu ba.

Koyarwar hadisin: Na kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su t…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · TSARKI · FIƘHU DA USULU · SHAFA A KAN HUFFI DA MAKAMANTANSA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah