Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Na kasance mutum ne mai yawan maziyyi, na kasance ina jin kunyar tambayar Annabi - tsira d…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عَنْ عَلِيٍّ رضي الله عنه قَالَ: كُنْتُ رَجُلًا مَذَّاءً وَكُنْتُ أَسْتَحْيِي أَنْ أَسْأَلَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِمَكَانِ ابْنَتِهِ فَأَمَرْتُ الْمِقْدَادَ بْنَ الْأَسْوَدِ فَسَأَلَهُ فَقَالَ: «يَغْسِلُ ذَكَرَهُ وَيَتَوَضَّأُ».
وَلِلبُخَاريِّ: فَقَالَ: «تَوَضَّأْ وَاغْسِلْ ذَكَرَكَ».
Aliyu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa ya kasance da yawan maziyyi yana fita daga gare shi - shi wani ruwa ne fari siriri mai zuba yana fita daga gaba a yayin sha'awa ko kafin jima'ai -. Bai san me zai aikata ba idan ya fita ba, sai ya ji kunyar ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa shi mijin Fadimatu ne 'yar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Sai ya bukaci Mikdad Dan Aswad ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da hakan, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya amsa masa da ya wanke gabansa sannan ya yi alwala.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · TSARKI · FIƘHU DA USULU · GUSAR DA NAJASA