Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > sai ya yi musu alwala irin alwalar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare …
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عَنْ يحيى بنِ عُمَارةَ المَازِنِيِّ قَالَ: شَهِدْتُ عَمْرَو بْنَ أَبِي حَسَنٍ سَأَلَ عَبْدَ اللَّهِ بْنَ زَيْدٍ، عَنْ وُضُوءِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَدَعَا بِتَوْرٍ مِنْ مَاءٍ، فَتَوَضَّأَ لَهُمْ وُضُوءَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَكْفَأَ عَلَى يَدِهِ مِنَ التَّوْرِ، فَغَسَلَ يَدَيْهِ ثَلاَثًا، ثُمَّ أَدْخَلَ يَدَهُ فِي التَّوْرِ، فَمَضْمَضَ وَاسْتَنْشَقَ وَاسْتَنْثَرَ، ثَلاَثَ غَرَفَاتٍ، ثُمَّ أَدْخَلَ يَدَهُ فَغَسَلَ وَجْهَهُ ثَلاَثًا، ثُمَّ غَسَلَ يَدَيْهِ مَرَّتَيْنِ إِلَى المِرْفَقَيْنِ، ثُمَّ أَدْخَلَ يَدَهُ فَمَسَحَ رَأْسَهُ، فَأَقْبَلَ بِهِمَا وَأَدْبَرَ مَرَّةً وَاحِدَةً، ثُمَّ غَسَلَ رِجْلَيْهِ إِلَى الكَعْبَيْنِ.
Abdullahi Dan Zaid - Allah Ya yarda da shi - yana bayyana siffar alwalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi a aikace, sai ya nemi karamar kwarya (buta) ta ruwa, a farko sai ya fara da wanke tafukansa, sannan ya karkatar da kwaryar ya zuba ruwa sai ya wankesu sau uku a wajen kwaryar, sannan ya shigar da hannunsa a cikin kwaryar ya kanfato daga gareta kanfata uku yana kuskurar baki a kowacce kanfata yana shaka ruwa yana facewa, sannan ya kanfato daga kwaryar (butar) sai ya wanke fuskarsa sau uku, sannan ya kanfato daga gareta sai ya wanke hannayensa zuwa gwiwoyin hannaye sau biyu-biyu, sannan ya shigar da hannayensa cikin kwaryar, ya shafi kansa da hannayensa ya fara da magabacin kansa har ya kai zuwa keyarsa saman wuya, sannan ya dawo da su har ya kai gurin da ya fara daga gare shi, sannan ya wanke kafafuwansa tare da idan sawu.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · TSARKI · FIƘHU DA USULU · ALWALA · SIFFAR ALWALA