Lallai Allah yayi Umarni ga Manzonsa kuma baiyi Umarni ga ku ba, kuma nima din anyi mun Iz…

Musulunci > Ha > Hadith > Daawa da hisba > Lallai Allah yayi Umarni ga Manzonsa kuma baiyi Umarni ga ku ba, kuma nima din anyi mun Iz…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 3

Rubutun hadisin: Lallai Allah yayi Umarni ga Manzonsa kuma baiyi Umarni…

عن أبي شُريح -خُوَيْلِدِ بن عمرو الخُزَاعي العدوي رضي الله عنه-: أنه قال لعمرو بن سعيد بن العاص -وهو يبعث الْبُعُوثَ إلى مكة- ائْذَنْ لي أيها الأمير أن أُحَدِّثَكَ قولا قام به رسول الله صلى الله عليه وسلم الغد من يوم الفتح؛ فسمعَتْه أُذُنَايَ ، وَوَعَاهُ قلبي، وأبصرته عيناي حين تكلم به أنه حمد الله وأثنى عليه، ثم قال: «إن مكة حَرَّمَهَا الله تعالى، ولم يُحَرِّمْهَا الناس، فلا يحل لِامْرِئٍ يؤمن بالله واليوم الآخر: أن يسفك بها دمًا، ولا يعضد بها شجرة، فإن أحد ترخص بقتال رسول الله صلى الله عليه وسلم فقولوا: إنَّ الله أذِن لرسوله ولم يأذن لكم. وإنما أذِنَ لي ساعة من نهار، وقد عادت حُرْمَتُهَا اليوم كَحُرمتها بالأمْسِ، فَلْيُبْلِغِ الشَّاهِدُ الغائب».
فقيل لأبي شريح: ما قال لك؟ قال: أنا أعلم بذلك منك يا أبا شريح، إن الحرم لَا يُعِيذُ عاصيا، وَلَا فَارًّا بدمٍ، ولَا فَارًّا بِخَرْبَةٍ.

Bayanin hadisin: Lallai Allah yayi Umarni ga Manzonsa kuma baiyi Umarni…

Kuma yayin da Amr Dan Sa'ad Da Asw, wanda aka fi sani da Al'ashdaq, cewa ya shirya runduna zuwa Makka Mai Alfarma kuma a lokacin yana sarki ne a Madina don ya yaki Abdullahi Dan Zubair sai Abu Shuraih ya zo masa, Khuwailid Dan Amr Alkhuza'i, don yayi masa Nasiha kan hakan. to sabida kasancewar wanda za'a yi wa nasihar yanajin kansa sai Abu Shuraih ya tausasa murya a gares hi, don Hikimarsa da kuma dora shi kan daidai don Nasihar tasa ta samu gurbin karba, da kuma karshen yayi kyau, sai ya nemi ayi masa ison ganin nasadon yi masa Nasiha a al'amarin kan rundunar da zzai aika, kuma ya bashi labarin cewa shi yana da tabbacin abinda zai gaya masa, kuma ya kafa dalili da cewa shi yaji wannan abu ne da kunnensa kuma ya rike shi a cikin zuciyarsa, kuma idonsa yaga lokacin da Annabi yake fadarsa, sai Amr Dan Sa'id yayi masa izinin yin Magana. Sai Abu Shuraih ya ce: Lallai cewa Annabi a Safiyar ranar bude makka ""cewa shi ya godewa Allah kuma yabi Ubangiji sannan ya ce: Lallai Makka Allah ya Haramta taTun lokacin da ya halicci sammai da kasa" kuma tana nan a girmamae da kuma tsarkinta, kuma amma mutane basu haramta ta ba kamar yadda suka haramta makiyaya wacce take ta dan wani lokaci ba da kuma wurin kiwo da shan ruwan dabbobi, kuma cewa Allah ne da kansa ya jibanci Haramtawar, don ya kasance mafi girma da kuma isa wajen haramcin to idan idan haramcin ya kasance tsoho haka kuma daga Allah ya ke to bazai halatta ga wani Mutum ba da yayi imani da Allah da kuma ranar lahira kuma indai yana kishin Imaninsa ya zubar da da Jini ko kuma ya sare bishiyarta, kuma idan wani wani yai iinin yaki na a ranar bude Makka, to ai shi ba kamar Manzon Allah ba ne, kuma shi anyi masa Izini amma kai ai ba'a maka ba.kuma cewa lallai ai bai halatta a Yaketa ba ko yaushe, kuma hakan ma ya faru ne wani Dan lokaci na rana sabida waccan bukatar, kuma haramcinta ya kuma dawowakamar yadda yake to duk wanda yaji ya gayawa wanda baiji ba, don wannan ne ya kai wannan Sarki nake isar maka da wannan sakon don ni sheda ne akan wannan Maganar, safiyar Ranar bude Makkah kuma kai baka nan akai, Sai Mutane suka ce Da Abu Shuraih :dame ya amsa maka Amr din ?sai ya ce ya amsamun da cewa "Nafi ka Sanin Wannan Kai Abu Shuraih , Lallai cewa ai Harami baya Kare Mai laifi, ko kuma wanda ya gudo cikinsa bayan yayi barna" Taisir Allam (Shafi na:381) da Tanbih Al'afham (3/519,510) da kuma Ta'asisu Al'ahkam.

Rukunan : UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DAGA MUMMUNA · LADUBBAN UMARNI DA KYAKKYAWAN AIKI DA HANI DAGA MUMMUNA · DA'AWA DA HISBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الحمد لله Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah