Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mu…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mu…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da a…

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَدْعُو وَيَقُولُ: «اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ القَبْرِ، وَمِنْ عَذَابِ النَّارِ، وَمِنْ فِتْنَةِ المَحْيَا وَالمَمَاتِ، وَمِنْ فِتْنَةِ المَسِيحِ الدَّجَّالِ».
وفِي لَفْظٍ لِمُسْلِمٍ: «إِذَا فَرَغَ أَحَدُكُمْ مِنَ التَّشَهُّدِ الْآخِرِ، فَلْيَتَعَوَّذْ بِاللهِ مِنْ أَرْبَعٍ: مِنْ عَذَابِ جَهَنَّمَ، وَمِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ، وَمِنْ فِتْنَةِ الْمَحْيَا وَالْمَمَاتِ، وَمِنْ شَرِّ الْمَسِيحِ الدَّجَّالِ».

Bayanin hadisin: Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da a…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana neman tsarin Allah daga abubuwa hudu bayan tahiyar karshe kuma kafin sallama a sallah, ya kuma umarcemu mu nemi tsarin Allah daga garesu,

Na farko: Daga azabar kabari.

Na biyu: Daga azabar wuta hakan a ranar Alkiyama .

Na uku: Daga fitinar rayuwa na sha'awowin duniya haramtattu da kuma shubuhohi masu batarwa, da kuma fitinar mutuwa, wato lokacin fitar rai, na karkacewa daga musulunci ko sunna, ko fitinar kabari kamar tambayar Mala'iku biyu.

Na hudu: Fitinar mai yawan yawo makaryaci (Dajjal) wanda zai fito a karshen zamani, Allah zai jarrabi bayinSa da shi, ya kebance shi da ambato dan girman fitinarsa da batarwarsa.

Koyarwar hadisin: Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da a…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · ZIKIRAN SALLAH

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah