Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a baya…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a baya…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gar…

عَنْ ‌وَرَّادٍ كَاتِبِ الْمُغِيرَةِ بْنِ شُعْبَةَ قَالَ: أَمْلَى عَلَيَّ الْمُغِيرَةُ بْنُ شُعْبَةَ فِي كِتَابٍ إِلَى مُعَاوِيَةَ: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَقُولُ فِي دُبُرِ كُلِّ صَلَاةٍ مَكْتُوبَةٍ: «لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، اللَّهُمَّ لَا مَانِعَ لِمَا أَعْطَيْتَ، وَلَا مُعْطِيَ لِمَا مَنَعْتَ، وَلَا يَنْفَعُ ذَا الْجَدِّ مِنْكَ الْجَدُّ».

Bayanin hadisin: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gar…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a bayan kowacce sallar farilla: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake ba Shi da abokin tarayya, mulki nasa ne, godiya ta tabbata a gareShi, Shi mai iko ne a kan dukkan komai, ya Allah ba mai hana abin da Ka bayar, kuma ba mai bayar da abin da Ka hana, kuma mai wadata wadatarsa ba ta amfanar da shi (komai) a wajenKa".

Wato: Ina tabbatar da kalmar tauhidi babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ibada ta gaskiya ina tabbatar da ita ga Allah, kuma ina koreta daga waninSa, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina tabbatar da cewa mulki na haƙiƙa cikakke na Allah ne, dukkanin godiyar wadanda ke sammai da ƙasa abar cancanta ce ga Allah - Maɗaukakin sarki -, yayin da yake Shi mai iko ne a kan dukkan komai, kuma abin da Allah Ya kaddara shi na bayarwa ko hanawa ba mai juyar da shi, kuma a wajenSa wadata ba ta amfanar da ma'abocinta, kaɗai aikinsa nagari ne zai amfanar da shi.

Koyarwar hadisin: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gar…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · ZIKIRAN SALLAH

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah