Kara Ruku'u 274 na Alkur'ani

Ruku'u 274 daga Surah Ta-Ha ne (ayoyi 90 zuwa 104). Yana ɗauke da ayoyi 15 kuma yana cikin Juz 16.

An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34

Ruku 274 a cikin Alkur'ani

15
ayoyi
1
Surah
16
Juz
v.90 – v.104
Ayoyi

Surori a cikin Ruku 274

طه · Juz 16
Kewaya
Alamomi
Sauti
Hadda
Nuni
Shafi 318
◄ Ruku'u 274 ►
سورة طه
Juz 16 82.9% (223/269)
Hizb 32 65.9% (89/135)

وَلَقَدْ قَالَ لَهُمْ هَـٰرُونُ مِن قَبْلُ يَـٰقَوْمِ إِنَّمَا فُتِنتُم بِهِۦ ۖ وَإِنَّ رَبَّكُمُ ٱلرَّحْمَـٰنُ فَٱتَّبِعُونِى وَأَطِيعُوٓا۟ أَمْرِى ﴿90﴾

Kuma, haƙĩƙa, Hãrũna yã ce musu daga gabãni, "Yã mutãnẽna! Lalle an fitinẽ ku da shi ne kawai. Kuma lalle Ubangijinku Mai rahama ne, sai ku bi ni, kuma ku yi ɗã'ã ga umurnĩna."

قَالُوا۟ لَن نَّبْرَحَ عَلَيْهِ عَـٰكِفِينَ حَتَّىٰ يَرْجِعَ إِلَيْنَا مُوسَىٰ ﴿91﴾

Suka ce: "Ba zã mu gushe ba faufau a kansa munã mãsu lazimta, sai Mũsã ya kõmo zuwa gare mu."

قَالَ يَـٰهَـٰرُونُ مَا مَنَعَكَ إِذْ رَأَيْتَهُمْ ضَلُّوٓا۟ ﴿92﴾

(Mũsã) ya ce: "Yã Hãrũna! Mẽ ya hane ka, sa'ad da kagan su sun ɓace."

أَلَّا تَتَّبِعَنِ ۖ أَفَعَصَيْتَ أَمْرِى ﴿93﴾

"Ba ka bĩ ni ba! Shin, to, ka sãɓã wa umurnina ne?"

قَالَ يَبْنَؤُمَّ لَا تَأْخُذْ بِلِحْيَتِى وَلَا بِرَأْسِىٓ ۖ إِنِّى خَشِيتُ أَن تَقُولَ فَرَّقْتَ بَيْنَ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ وَلَمْ تَرْقُبْ قَوْلِى ﴿94﴾

(Hãrũna) ya ce: "Yã ɗãn'uwãna! Kada ka yi kãmu ga gẽmũna kõ ga kaina. Lalle nĩ, nã ji tsõron ka ce: Ka rarraba a tsakãnin Banĩ Isrã'ĩla kuma ba ka tsare maganata ba."

قَالَ فَمَا خَطْبُكَ يَـٰسَـٰمِرِىُّ ﴿95﴾

(Mũsã) ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinka? Ya Sãmiri!"

قَالَ بَصُرْتُ بِمَا لَمْ يَبْصُرُوا۟ بِهِۦ فَقَبَضْتُ قَبْضَةًۭ مِّنْ أَثَرِ ٱلرَّسُولِ فَنَبَذْتُهَا وَكَذَٰلِكَ سَوَّلَتْ لِى نَفْسِى ﴿96﴾

(Sãmiri) ya ce: "Nã ga abin da ba su gan shi ba shi, sai na yi damƙa, damƙa guda daga kufan sãwun Manzon, sa'an nan na jẽfa ta. Kuma haka dai raina ya ƙawãta mini."

قَالَ فَٱذْهَبْ فَإِنَّ لَكَ فِى ٱلْحَيَوٰةِ أَن تَقُولَ لَا مِسَاسَ ۖ وَإِنَّ لَكَ مَوْعِدًۭا لَّن تُخْلَفَهُۥ ۖ وَٱنظُرْ إِلَىٰٓ إِلَـٰهِكَ ٱلَّذِى ظَلْتَ عَلَيْهِ عَاكِفًۭا ۖ لَّنُحَرِّقَنَّهُۥ ثُمَّ لَنَنسِفَنَّهُۥ فِى ٱلْيَمِّ نَسْفًا ﴿97﴾

(Mũsã) ya ce: "To, ka tafi, sabõda haka lalle ne kanã da a cikin rãyuwarka, ka ce 'Bãbu shãfa' kuma kanã da wani ma'alkawarta, bã zã a sãɓa maka gare ta ba. Kuma ka dũba zuwa ga gunkinka wanda ka yini a kansa kanã mai lazimta. Lalle ne muna ƙõne shi, sa'an nan kuma munã shẽƙe shi, a cikin tẽku, shẽƙẽwa."

إِنَّمَآ إِلَـٰهُكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِى لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ۚ وَسِعَ كُلَّ شَىْءٍ عِلْمًۭا ﴿98﴾

Abin sani kawai abin bautãwarku Allah kawai ne wanda bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi kuma Yã yalwaci dukkan kõme da ilmi.

كَذَٰلِكَ نَقُصُّ عَلَيْكَ مِنْ أَنۢبَآءِ مَا قَدْ سَبَقَ ۚ وَقَدْ ءَاتَيْنَـٰكَ مِن لَّدُنَّا ذِكْرًۭا ﴿99﴾

Kamar wancan ne Muke lãbartãwa a gare ka, daga lãbãran abin da ya gabãta, alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun bã ka zikiri (Alƙur'ãni) daga gunMu.

مَّنْ أَعْرَضَ عَنْهُ فَإِنَّهُۥ يَحْمِلُ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ وِزْرًا ﴿100﴾

Wanda ya kau da kai daga gare shi, to, lalle shĩ, yanãɗaukar wani nauyi a Rãnar ¡iyãma.

خَـٰلِدِينَ فِيهِ ۖ وَسَآءَ لَهُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ حِمْلًۭا ﴿101﴾

Sunã madawwama a cikinsa, kuma yã mũnana ya zama abin ɗauka, a Rãnar ¡iyãma.

يَوْمَ يُنفَخُ فِى ٱلصُّورِ ۚ وَنَحْشُرُ ٱلْمُجْرِمِينَ يَوْمَئِذٍۢ زُرْقًۭا ﴿102﴾

A Rãnar da ake hũrãwa a cikin ƙãho kuma Munã tãra mãsu laifi, a rãnar nan, sunã mãsu shũɗãyen idãnu.

يَتَخَـٰفَتُونَ بَيْنَهُمْ إِن لَّبِثْتُمْ إِلَّا عَشْرًۭا ﴿103﴾

Suna ɓõye magana a tsakãninsu, (Sunã ce wa jũna) "Ba ku zauna ba (a cikin dũniya) fãce kwãna gõma."

نَّحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَقُولُونَ إِذْ يَقُولُ أَمْثَلُهُمْ طَرِيقَةً إِن لَّبِثْتُمْ إِلَّا يَوْمًۭا ﴿104﴾

Mu ne mafi sani ga abin da suke faɗa a sa'ad da mafĩficinsu ga hanya ke cẽwa, "Ba ku zauna ba fãce a yini guda."

بسم الله الرحمن الرحيم Jum 26 Rabi' al-Thani
الجمعة 26 ربيع الآخر
هلال متناقص Gajimaren Raguwa Rana 27.7 / 29.5
Haske 4%
Wata Sabo a cikin kwana 2
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah