Kara Ruku'u 524 na Alkur'ani

Ruku'u 524 daga Surah Al-Infitar ne (ayoyi 1 zuwa 19). Yana ɗauke da ayoyi 19 kuma yana cikin Juz 30.

An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34

Ruku 524 a cikin Alkur'ani

19
ayoyi
1
Surah
30
Juz
v.1 – v.19
Ayoyi
الإنفطار · Juz 30
Kewaya
Alamomi
Sauti
Hadda
Nuni
Shafi 587
◄ Ruku'u 524 ►
سورة الإنفطار
Juz 30 27.8% (157/564)
Hizb 59 56.9% (157/276)

إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنفَطَرَتْ ﴿1﴾

Idan sama ta tsãge.

وَإِذَا ٱلْكَوَاكِبُ ٱنتَثَرَتْ ﴿2﴾

Kuma idan taurãri suka wãtse.

وَإِذَا ٱلْبِحَارُ فُجِّرَتْ ﴿3﴾

Kuma idan tẽkuna aka facce su.

وَإِذَا ٱلْقُبُورُ بُعْثِرَتْ ﴿4﴾

Kuma idan kaburbura aka tõne su.

عَلِمَتْ نَفْسٌۭ مَّا قَدَّمَتْ وَأَخَّرَتْ ﴿5﴾

Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْإِنسَـٰنُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ ٱلْكَرِيمِ ﴿6﴾

Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.

ٱلَّذِى خَلَقَكَ فَسَوَّىٰكَ فَعَدَلَكَ ﴿7﴾

Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.

فِىٓ أَىِّ صُورَةٍۢ مَّا شَآءَ رَكَّبَكَ ﴿8﴾

A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.

كَلَّا بَلْ تُكَذِّبُونَ بِٱلدِّينِ ﴿9﴾

A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!

وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَـٰفِظِينَ ﴿10﴾

Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.

كِرَامًۭا كَـٰتِبِينَ ﴿11﴾

Mãsu daraja, marubũta.

يَعْلَمُونَ مَا تَفْعَلُونَ ﴿12﴾

Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.

إِنَّ ٱلْأَبْرَارَ لَفِى نَعِيمٍۢ ﴿13﴾

Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.

وَإِنَّ ٱلْفُجَّارَ لَفِى جَحِيمٍۢ ﴿14﴾

Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.

يَصْلَوْنَهَا يَوْمَ ٱلدِّينِ ﴿15﴾

Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.

وَمَا هُمْ عَنْهَا بِغَآئِبِينَ ﴿16﴾

Bã zã su faku daga gare ta ba.

وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلدِّينِ ﴿17﴾

Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako?

ثُمَّ مَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلدِّينِ ﴿18﴾

Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?

يَوْمَ لَا تَمْلِكُ نَفْسٌۭ لِّنَفْسٍۢ شَيْـًۭٔا ۖ وَٱلْأَمْرُ يَوْمَئِذٍۢ لِّلَّهِ ﴿19﴾

Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.

بسم الله الرحمن الرحيم Alh 25 Rabi' al-Thani
الخميس 25 ربيع الآخر
هلال متناقص Gajimaren Raguwa Rana 26.9 / 29.5
Haske 8%
Wata Sabo a cikin kwana 3
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah