Kara Shafi 494 na Alkur'ani

Shafi 494 na Mushaf yana ɗauke da ayoyi 13. Yana cikin Juz 25, Hizb 50.

An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34

Shafi 494 a cikin Alkur'ani

13
ayoyi
25
Juz
50
Hizb
1
Surah

Surori a cikin Shafi 494

الزخرف · Juz 25
Juz 25
Shafi 494
سورة الزخرف
Juz 25 49.2% (121/246)
Hizb 50 22.8% (37/162)

وَإِنَّهُۥ لَعِلْمٌۭ لِّلسَّاعَةِ فَلَا تَمْتَرُنَّ بِهَا وَٱتَّبِعُونِ ۚ هَـٰذَا صِرَٰطٌۭ مُّسْتَقِيمٌۭ ﴿٦١﴾

Kuma lalle shĩ, haƙĩƙa, wani ilmi ne na Sa'a, sabõda haka, kada ku yi shakka a gare ta, kuma ku bĩ Ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.

وَلَا يَصُدَّنَّكُمُ ٱلشَّيْطَـٰنُ ۖ إِنَّهُۥ لَكُمْ عَدُوٌّۭ مُّبِينٌۭ ﴿٦٢﴾

Kuma kada Shaiɗan ya taushe ku (daga hanyar). Lalle shĩ maƙiyi ne a gare ku, mai bayyanãwar ƙiyayya.

وَلَمَّا جَآءَ عِيسَىٰ بِٱلْبَيِّنَـٰتِ قَالَ قَدْ جِئْتُكُم بِٱلْحِكْمَةِ وَلِأُبَيِّنَ لَكُم بَعْضَ ٱلَّذِى تَخْتَلِفُونَ فِيهِ ۖ فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ ﴿٦٣﴾

Kuma a lõkacin da Ĩsã ya jẽ da hujjõji bayyanannu, ya ce: "Lalle ne nã zo muku da hikima kuma dõmin in bayyana muku, sãshen abin da kuke sãɓã wa jũna acikinsa, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'a."

إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ رَبِّى وَرَبُّكُمْ فَٱعْبُدُوهُ ۚ هَـٰذَا صِرَٰطٌۭ مُّسْتَقِيمٌۭ ﴿٦٤﴾

"Lalle ne, Allah Shĩ ne Ubangijina kuma Shi ne Ubangijinku sabõda haka ku bauta Masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya."

فَٱخْتَلَفَ ٱلْأَحْزَابُ مِنۢ بَيْنِهِمْ ۖ فَوَيْلٌۭ لِّلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ مِنْ عَذَابِ يَوْمٍ أَلِيمٍ ﴿٦٥﴾

Sai ƙungiyõyi suka sãɓa a tsakãninsu. To, bone yã tabbata ga waɗanda suka yi zãlunci daga azãbar yini mai raɗaɗi!

هَلْ يَنظُرُونَ إِلَّا ٱلسَّاعَةَ أَن تَأْتِيَهُم بَغْتَةًۭ وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ ﴿٦٦﴾

Shin sunã jiran wani abu ne? sai dai Sa'a ta jẽ musu bisaga abke, alhãli kuwa ba su sani ba.

ٱلْأَخِلَّآءُ يَوْمَئِذٍۭ بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ عَدُوٌّ إِلَّا ٱلْمُتَّقِينَ ﴿٦٧﴾

Masõya a yinin nan, sãshensu zuwa ga sãshe maƙiya ne, fãce mãsu taƙawa (sũ kam mãsu son jũna ne).

يَـٰعِبَادِ لَا خَوْفٌ عَلَيْكُمُ ٱلْيَوْمَ وَلَآ أَنتُمْ تَحْزَنُونَ ﴿٦٨﴾

Ya bãyĩNa! Bãbu tsõro a kanku a yau, kuma bã zã ku yi baƙin ciki ba.

ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا وَكَانُوا۟ مُسْلِمِينَ ﴿٦٩﴾

Waɗanda suka yi ĩmãni da ãyõyinMu, kuma suka kasance mãsu sallamawar al'amari (ga Allah).

ٱدْخُلُوا۟ ٱلْجَنَّةَ أَنتُمْ وَأَزْوَٰجُكُمْ تُحْبَرُونَ ﴿٧٠﴾

Ku shiga Aljanna, kũ da mãtan aurenku, anã girmama ku.

يُطَافُ عَلَيْهِم بِصِحَافٍۢ مِّن ذَهَبٍۢ وَأَكْوَابٍۢ ۖ وَفِيهَا مَا تَشْتَهِيهِ ٱلْأَنفُسُ وَتَلَذُّ ٱلْأَعْيُنُ ۖ وَأَنتُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ ﴿٧١﴾

Anã kẽwayãwa a kansu da akussa na zĩnãriya da kõfuna, alhãli kuwa a cikinsu akwai abin da rãyuka ke marmari kuma idãnu su ji dãɗi, kuma kũ, a cikinta (Aljannar), madawwama ne.

وَتِلْكَ ٱلْجَنَّةُ ٱلَّتِىٓ أُورِثْتُمُوهَا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ ﴿٧٢﴾

Kuma waccan ita ce Aljannar, wannan da aka gãdar da ku ita sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa.

لَكُمْ فِيهَا فَـٰكِهَةٌۭ كَثِيرَةٌۭ مِّنْهَا تَأْكُلُونَ ﴿٧٣﴾

Kunã sãmu, a cikinta, 'yã'yan itãcen marmari mãsu yawa, daga cikinsu kuke ci.

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 20 Safar
الأربعاء 20 صفر
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 21.9 / 29.5
Haske 52%
Wata Sabo a cikin kwana 8
سبحان الله Subhanallah - Tsarkin Allah