Kara Shafi 73 na Alkur'ani

Shafi 73 na Mushaf yana ɗauke da ayoyi 7. Yana cikin Juz 4, Hizb 8.

An sabunta a 28 Oktoba 2026 00h24

Shafi 73 a cikin Alkur'ani

7
ayoyi
4
Juz
8
Hizb
1
Surah

Surori a cikin Shafi 73

آل عمران · Juz 4
Kewaya
Alamomi
Sauti
Hadda
Nuni
Juz 4
◄ Shafi 73 ►
سورة آل عمران
Juz 4 61.8% (81/131)
Hizb 8 5.7% (3/53)

فَٱنقَلَبُوا۟ بِنِعْمَةٍۢ مِّنَ ٱللَّهِ وَفَضْلٍۢ لَّمْ يَمْسَسْهُمْ سُوٓءٌۭ وَٱتَّبَعُوا۟ رِضْوَٰنَ ٱللَّهِ ۗ وَٱللَّهُ ذُو فَضْلٍ عَظِيمٍ ﴿174﴾

Sa'an nan sukajũya da wata ni'ima daga Allah da wata falala, wata cũta ba ta shãfe su ba, kuma suka bi yardar Allah. Kuma Allah ne Ma'abucin falala Mai girma.

إِنَّمَا ذَٰلِكُمُ ٱلشَّيْطَـٰنُ يُخَوِّفُ أَوْلِيَآءَهُۥ فَلَا تَخَافُوهُمْ وَخَافُونِ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ ﴿175﴾

Wancan, Shaiɗan ne kawai yake tsõratar da, ku masõyansa. To, kada ku ji tsõronsu ku ji tsõro Na idãn kun kasance mãsu ĩmãni.

وَلَا يَحْزُنكَ ٱلَّذِينَ يُسَـٰرِعُونَ فِى ٱلْكُفْرِ ۚ إِنَّهُمْ لَن يَضُرُّوا۟ ٱللَّهَ شَيْـًۭٔا ۗ يُرِيدُ ٱللَّهُ أَلَّا يَجْعَلَ لَهُمْ حَظًّۭا فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ ﴿176﴾

Kuma waɗannan da suke gaugãwa a cikin kãfirci kada su ɓãta maka rai. Lalle ne su, bã zã su cũci Allah da kõme ba. Allah yanã nufin cẽwa, bã zai sanya musu wani rabo ba a cikin Lãhira kuma suna da wata azãba mai girma.

إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱشْتَرَوُا۟ ٱلْكُفْرَ بِٱلْإِيمَـٰنِ لَن يَضُرُّوا۟ ٱللَّهَ شَيْـًۭٔا وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌۭ ﴿177﴾

Lalle ne, waɗanda suka sayi kãfirci da ĩmani, ba zã su cũci Allah da kõme ba. Koma sunã da azãba mai raɗaɗi.

وَلَا يَحْسَبَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓا۟ أَنَّمَا نُمْلِى لَهُمْ خَيْرٌۭ لِّأَنفُسِهِمْ ۚ إِنَّمَا نُمْلِى لَهُمْ لِيَزْدَادُوٓا۟ إِثْمًۭا ۚ وَلَهُمْ عَذَابٌۭ مُّهِينٌۭ ﴿178﴾

Kuma kada waɗanda suka kãfirta su yi zaton cẽwa, lalle ne jinkirin da Muke yi musu alhẽri ne ga rãyukansu. Munã yi musu jinkirin ne dõmin su ƙãra laifi kawai kuma suna da azãba mai wulãƙantarwa.

مَّا كَانَ ٱللَّهُ لِيَذَرَ ٱلْمُؤْمِنِينَ عَلَىٰ مَآ أَنتُمْ عَلَيْهِ حَتَّىٰ يَمِيزَ ٱلْخَبِيثَ مِنَ ٱلطَّيِّبِ ۗ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُطْلِعَكُمْ عَلَى ٱلْغَيْبِ وَلَـٰكِنَّ ٱللَّهَ يَجْتَبِى مِن رُّسُلِهِۦ مَن يَشَآءُ ۖ فَـَٔامِنُوا۟ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦ ۚ وَإِن تُؤْمِنُوا۟ وَتَتَّقُوا۟ فَلَكُمْ أَجْرٌ عَظِيمٌۭ ﴿179﴾

Allah bai kasance yana barin mũminai a kan abin da kuke kansa ba, sai Ya rarrabe mummũna daga mai kyau. Kuma Al lah bai kasance Yanã sanar da ku gaibi ba. Kuma amma Allah Yana zãɓen wanda Ya so daga manzanninSa. Sabõda haka ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa Kuma idan kun yi ĩmãni kuma kuka yi taƙawa, to, kunã da lãdã mai girma.

وَلَا يَحْسَبَنَّ ٱلَّذِينَ يَبْخَلُونَ بِمَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضْلِهِۦ هُوَ خَيْرًۭا لَّهُم ۖ بَلْ هُوَ شَرٌّۭ لَّهُمْ ۖ سَيُطَوَّقُونَ مَا بَخِلُوا۟ بِهِۦ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۗ وَلِلَّهِ مِيرَٰثُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌۭ ﴿180﴾

Kuma kada waɗannan da suke yin rõwa da abin da Allah Ya bã su daga falalarSa su yi zaton shĩ ne mafi alhẽri a gare su A'a, shĩ mafi sharri ne a gare su. Zã a yi musu saƙandami da abin da suka yi rõwa da Shi a Rãnar ¡iyãma Kuma ga Allah gãdon sammai da ƙasa yake, kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 23 Jumada al-Awwal
الأربعاء 23 جمادى الأولى
التربيع الأخير Kwata na Ƙarshe Rana 23.9 / 29.5
Haske 32%
Wata Sabo a cikin kwana 6
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah