Cewa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan yana sallah y…
Musulunci > Ha > Hadith > Sira da tarihi > Cewa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan yana sallah y…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Cewa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare…
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مَالِكٍ ابْنِ بُحَيْنَةَ رضي الله عنه: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ إِذَا صَلَّى فَرَّجَ بَيْنَ يَدَيْهِ حَتَّى يَبْدُوَ بَيَاضُ إِبْطَيْهِ.
Bayanin hadisin: Cewa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare…
Tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya kasance idan zai yi sujjada yana buɗa tsakanin hannayensa a tsakiyar sujjada; sai kowanne hannu ya nisanta daga gefan da yake biye masa, kwatankwacin fukafukai biyu, har launin fatar hammatarsa ya bayyana; wannan yana daga kai matuƙa a nisantar da zira'i biyu da kuma nisantar da su daga sasanninsu.
Koyarwar hadisin: Cewa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare…
- An so wannan yanayin a cikin sujjada, shi ne nisantar da damatsansa biyu daga sasanninsa.
- Mamun da na kusa da shi yake cutuwa da nisantarwar to ba'a shar’anta masa hakan ba.
- Akwai hikimomi da fa'idoji masu yawa a cikin nisantar a cikin sujjada, daga cikinsu: Bayyanar da nishaɗi da kwaɗayi a cikin sallah, kuma idan ya dogara akan dukkan gaɓɓan sujjada sai kowacce gaɓa ta ɗauki haƙƙinta daga bauta. Akace: Hikima a cikin hakan ya yi kama da tawali'u, kuma mafi isuwa a cikin tabbatar da goshi da hanci a ƙasa, kuma dan banbance kowacce gaɓa da kanta.
Rukunan :
SIRAR ANNABI
· ƊABI'U IRIN NA (ANNABI) MUHAMMAD
· TSARIN ANNABI
· TSARINSA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI A SALLAH
· SIRA DA TARIHI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa