Za’a zo da mutum ranar Alkiyama, sai a jefa shi a cikin wuta, sai hanjin cikinsa su fita,…

Musulunci > Ha > Hadith > Abubuwa masu tausasa zukata da waazozi > Za’a zo da mutum ranar Alkiyama, sai a jefa shi a cikin wuta, sai hanjin cikinsa su fita,…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Za’a zo da mutum ranar Alkiyama, sai a jefa shi a ciki…

Bayanin hadisin: Za’a zo da mutum ranar Alkiyama, sai a jefa shi a ciki…

An cewa Usama ɗan Zaid Allah - Ya yarda da su - Shin baka shiga wurin Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - ba ka yi masa magana cikin abinda yake faruwa na fitina tsakanin mutane da kokari a kasheta gabaɗayanta, sai ya sananar da su cewa shi ya yi masa magana a sirri dan neman maslaha badan tada fitina ba, manufarsa cewa shi ba ya son bayyanar da inkari ga sarakuna a cikin jama'a, sai ya zama sababi na rena khalifa, kuma shi ne kofar fitina da sharri ba zan zama farkon wanda zai buɗeta ba.

Sannan Usama - Allah Ya yarda da su - ya ce: Shi yana yi wa sarakuna nasiha a boye kuma ba ya yi wa wani mujamala koda sarki ne, kuma ba ya yi musu fadanci sai ya yabe su a gabansu da karya, hakan bayan ya ji daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi za’a zo da wani mutum ranar alkiyama, sai a jefa shi a cikin wuta, sai hanjin (kayan) cikinsa su fito daga cikinsa da gaggawa saboda tsananin zafi da tsananin azaba, sai ya kewaya da 'ya'yan cikinsa yana wannan halin kamar kewayawar jaki a gefan dutsen nikansa, sai 'yan wuta su taru a gefansa kamar sarkar data kewaye shi, sai su tambaye shi : Ya wane, shin ba kaine ka kasance kana umartarmu da aikin alheri ba kuma kake hanamu abin ki ba?!

Sai ya ce: Lallai ni na kasance ina horo da aikin alheri amma bana aikata shi, kuma ina hani daga abin ki kuma ina aikata shi.

Koyarwar hadisin: Za’a zo da mutum ranar Alkiyama, sai a jefa shi a ciki…

Rukunan : ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · SIFFOFIN ALJANNA DA WUTA · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 17.2 / 29.5
Haske 94%
Wata Sabo a cikin kwana 12
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah