Musulunci > Ha > Hadith > Ladubba na sharia > Na ce: Ya Manzon Allah menene tsira? ya ce: "Ka mallaki harshenka gareka, kuma gidanka ya …
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1Uƙuba ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da sabubban tsirar mumini a duniya da lahira?
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Na horeka da al'amura uku:
Na farko: Ka kiyaye harshenka daga abinda babu alheri a cikinsa, daga faɗar kowane sharri, kuma kada ka yi wani furuci sai da alheri.
Na biyu: Ka lazimci gidanka dan ka bautawa Allah a cikin kaɗaitakarka, ka shagalta da biyayya ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, ka nisanci fitinu a cikin gidanka.
Na uku: Ka yi kuka ka yi nadama ka tuba daga abinda ka aikata na zunubai.
Rukunan : LADUBBA NA SHARI'A · ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · LADUBBAN MAGANA DA SHIRU · TUBA · FALALOLI DA LADUBBA