Dukkan wanda ya ɗosani wani yanki na ilimin taurari, to, haƙiƙa ya ɗosani wani yanki na ts…
Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Dukkan wanda ya ɗosani wani yanki na ilimin taurari, to, haƙiƙa ya ɗosani wani yanki na ts…
Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Dukkan wanda ya ɗosani wani yanki na ilimin taurari, to…
عن ابن عباس رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «من اقتبَسَ علْمًا مِنَ النُّجُومِ اقْتبَسَ شُعبَة مِن السِّحرِ، زادَ ما زادَ».
Bayanin hadisin: Dukkan wanda ya ɗosani wani yanki na ilimin taurari, to…
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana duk wanda ya koyi, ya samu wani tsagi na ilimin taurari da buruji da kuma kafa dalili da motsinsu da shigarsu da fitarsu a kan abin da zai faru a bayan ƙasa na mutuwar wane, ko rayuwarsa, ko rashin lafiyarsa, da makamancin haka cikin abinda zai faru nan gaba, to, haƙiƙa ya koyi wani tsagi na sihiri, kuma duk lokacin da mutum ya ƙara wannan ilimin, to, ya ƙara asiri [tsafi] ne.
Koyarwar hadisin: Dukkan wanda ya ɗosani wani yanki na ilimin taurari, to…
- Haramcin ilimin taurari wanda yake na ba da labarin abin da zai faru nan gaba, dogaro da yanayin taurari, domin yana cikin iƙirarin sanin gaibu.
- Ilimin taurari haramun ne, yana cikin nau’ukan asiri [tsafi] wanda yake kore Tauhidi, saɓanin nazarin taurari domin sanin inda mutum ya nufa, ko sanin alƙibla, ko sanin shigar lokacin wasu bukukuwa, ko watanni, to, wannan ya halatta.
- Duk lokacin da ya ƙara a koyar ilimin taurari, to, yana ƙara koyar wani kaso ne na asiri [tsafi].
- Taurari suna da fa'idoji uku, Allah ya ambace su a LittafinSa: Ƙawa ga sama, alamomi da za’a dinga ganewa da su, jifa ga shaiɗanu.
Rukunan :
ILIMIN AƘIDA
· SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE
· ABUBUWAN DA SUKE WARWARE MUSULUNCI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
اللهم صل على محمد
Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad