Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mini: «Ka yi mini karatu

Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mini: «Ka yi mini karatu

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -…

Bayanin hadisin: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi Abdullahi Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya karanta masa wani abu na Alƙur'ani, sai ya ce; Ya Manzon Allah, ta yaya zan karanta maka alhali kai aka saukarwa?! sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai ni ina son in ji shi daga wanina, sai ya karanta masa Suratu al-Nisa'i yayin da ya kai ga faɗinSa Allah - Maɗaukakin sarki -:{To yaya al'amarin zai kasance idan Muka zo da kowace al'umma tare da mai yi mata shaida, kai kuma Muka zo da kai a matsayin mai shaida akan waɗannan al'ummar?} Wato yaya halinka da halin al'ummarka zasu kasance idan Muka zo da kai kana mai shaida ga al'ummarka cewa kai ka isar musu da saƙo, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ka tsaya da karatun a yanzu, Ibnu Mas'uda - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Sai na juya wajensa sai ga idanuwansa suna zubar da hawaye dan tsoron mauƙifin (alƙiyama), da kuma tausayin al'ummarsa.

Koyarwar hadisin: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -…

Rukunan : ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA · BINCIKE-BINCIKE GAMAMMU NA ALƘUR'ANI · LADUBBAN KARATUN ALƘUR'ANI DA NA MAHADDATANSA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah