Mazon Allah -tsira da amincin Allah- ya ji hayaniyar rigima a kofar gidansa

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Mazon Allah -tsira da amincin Allah- ya ji hayaniyar rigima a kofar gidansa

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Mazon Allah -tsira da amincin Allah- ya ji hayaniyar ri…

عن أُمُّ سَلَمَة رضي الله عنها أن رسول الله صلى الله عليه وسلم سَمِعَ جَلَبَةَ خَصْمٍ بِبَابِ حُجْرَتِهِ، فَخَرَجَ إلَيْهِمْ، فقال: «ألا إنما أنا بشر، وإنما يأتيني الخصم، فلعل بعضكم أن يكون أبلغ من بعض؛ فَأَحْسِبُ أَنَّهُ صَادِقٌ؛ فَأَقْضِي لَهُ، فمن قضيت له بحق مسلم فإنما هي قطعة من نار، فَلْيَحْمِلْهَا أَوْ يَذَرْهَا».

Bayanin hadisin: Mazon Allah -tsira da amincin Allah- ya ji hayaniyar ri…

Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ji hayaniyar masu rigima,a kofar gidansa,sai ya fito don ya yi musu hukunci a tsakanin su sai yace: Lallai Ni mutum ne kamar ku, ban san gaibu ba, bana bada labarin boyayyayun al'amura, ban san waye mai gaskiya ko makaryaci a cikinku ba, masu rigima sukan zo dan na yi hikunci a tsakaninsu,kuma hukunci na yana kasancewa ne akan abin da na ji daga kowane bangare, da rantsuwoyinsu, kuma yana iya kasancewa wani yafi wani iya magana sai na zaci shi ne mai gaskiya sai na bashi gaskiya,tare da cewa abokin fadan shi ne mai gaskiya, ku sani ina hukunci da abubuwan da suke bayyane ne ba da wanda suke boye ba, ba zai halarta haram ba, don haka duk wanda na bawa gaskiya alhali ya san shi ne marar gaskiya, to yasan cewa wani yanki na wuta ne na yanko masa, in ya so sai ya dauka ko ya bari, sakamakon hakan na komawa akansa, Allah na jiran azzalumai a madakata

Rukunan : ALƘALANCI · ƘARARRAKI DA SHEDU · FIƘHU DA USULU

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah