Wallahi ɗayanku ba zai ɗauki wani abu ba, ba tare da haƙƙinsa ba sai ya haɗu da Allah yana…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na muamalat > Wallahi ɗayanku ba zai ɗauki wani abu ba, ba tare da haƙƙinsa ba sai ya haɗu da Allah yana…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Wallahi ɗayanku ba zai ɗauki wani abu ba, ba tare da ha…

Bayanin hadisin: Wallahi ɗayanku ba zai ɗauki wani abu ba, ba tare da ha…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ɗorawa wani mutum aiki ana ce masa: Ibnul Lutbiyyah, shi ne aikin tattaro zakka daga ƙabilar Banu Sulaim, lokacin da ya dawo Madina sai ya yi masa bayani akan abinda ya karɓa da kuma abinda ya yi amfani da shi, sai Ibnul Lutbiyyah ya ce: Wannan dukiyarku ce wacce na tattarota ta zakka, wannan dukiyar kuma anbani kyautarta ne. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Shin ba zaka zauna acikin gidan babanka da babarka ba ka duba ka gani shin za’a baka kyautar idan kai mai gaskiya ne; domin cewa haƙƙoƙin da ka yi aiki saboda su sune sababin baka kyauta, kuma da a ce ka zauna a cikin gidanka da ba'a baka kyautar komai ba, dan haka ba ya kamata gareka ka halartata saboda kawai ta sameka ta hanyar kyauta. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya hau minbari yana mai yin huɗuba alhali shi yana mai fushi, sai ya godewa Allah kuma ya yi yabo gare shi, sannan ya ce: Bayan haka lallai ni ina ɗorawa ɗayanku aiki akan abinda Allah Ya sanya mini tasarrufi a cikinsa na zakka da kuma ganimomi, sai wanda ya yi aikin ya zo, ya ce: Wannan naku ne wannan kuma kyauta ce da aka bani! Shin ba ya zauna a cikin gidan babansa da babarsa ba har kyautarsa ta zo masa, wallahi wani ba zai ɗauki wani abu ba daga abinda aka ba shi, ba tare da haƙƙinsa ba sai ya haɗu da Allah yana ɗauke da shi a ranar alƙiyama akan wuyansa, idan abinda ya ɗauka raƙumi ne yana kukan raƙuma, ko saniya ce da take irin kukan shanu, ko akuya ce da take irin kukan akuyoyi. Sannan ya ɗaga hannayensa sosai har waɗanda ke zaune suka ga farin hammatarsa, sannan ya ce: Ya Allah na isar musu da hukuncin Allah. Sannan Abu Humaid al-Sa'idi - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa: Wannan abinda idona ya gani ne kuma kunnena ya ji shi.

Koyarwar hadisin: Wallahi ɗayanku ba zai ɗauki wani abu ba, ba tare da ha…

Rukunan : FIƘHU NA MU'AMALAT · KYAUTA DA KYAUTA · SIYASA A SHARI'ANCE · AYYUKAN DA SUKE KAN SHUGABA · FIƘHU DA USULU · DA'AWA DA HISBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
سبحان الله وبحمده Tsarkin Allah da godiyarSa

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah