Babu cuta mai yaɗuwa zuwa ga wani (da karantanta) babu canfi, ko mujiya, ko Safar, kuma ka…

Musulunci > Ha > Hadith > Abubuwa masu tausasa zukata da waazozi > Babu cuta mai yaɗuwa zuwa ga wani (da karantanta) babu canfi, ko mujiya, ko Safar, kuma ka…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Babu cuta mai yaɗuwa zuwa ga wani (da karantanta) babu…

Bayanin hadisin: Babu cuta mai yaɗuwa zuwa ga wani (da karantanta) babu…

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana sashin al'amuran Jahiliyya (maguzawa) dan gargaɗi daga gare su, da kuma bayanin al'amari yana hannun Allah, kuma wani abu ba ya kasancewa sai da umarninSa da ƙaddarawarSa, su ne:

Na farko: Mutanen Jahiliyya sun kasance suna zatan cewa cuta tana yaɗuwa da kanta; sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga ƙudirce tashin cuta daga mara lafiya zuwa ga mai lafiya da ɗabi'arta; Allah Shi ne Mai tasarrufi a cikin kasantattu; kuma Shi ne wanda Yake saukar da cuta kuma Yake ɗauketa, hakan ba ya faruwa saida nufinSa da ƙaddarawarSa.

Na biyu: Mutanen Jahiliyya sun kasance idan sun fita dan wata tafiya ko kasuwanci, sai su yi wa tsuntsu tsawa, idan ya tashi ɓangaren dama sai su yi murna, idan ya tashi ɓangaren hagu sai su canfa su dawo, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga wannan canfin da tsuntsu, ya kuma bayyana cewa hakan akida ce ɓatacciya.

Na uku: Mutanen Jahiliyya sun kasance suna cewa: Idan mujiya ta faɗo a kan wani gida sai musiba ta samu mutanen wannan gidan; sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani game da canfa hakan.

Na huɗu: Ya yi hani daga canfa watan Safar, shi ne wata na biyu daga watannin ƙamariyya. (Wasu kuma) suka ce Safar shi ne: Wata micijiya ce da take a ciki tana samun dabbobi da mutane, suna riya cewa ita ce mafi tsananin yaɗuwa daga cutar kirci; sai ya kore wannan akidar.

Na biyar: Ya yi umarni da nisantar wanda aka shafa da cutar kuturta kamar yadda zaka nisanci zaki, hakan dan bai wa kai kariya da kuma nema masa kuɓuta da kuma aikata sabubban da Allah ya yi umarni da su. Kuturta: Wata cuta ce da gaɓɓan mutum suke cin juna daga gareta.

Koyarwar hadisin: Babu cuta mai yaɗuwa zuwa ga wani (da karantanta) babu…

Rukunan : ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · ILIMIN AƘIDA · AYYUKAN ZUKATA · FALALOLI DA LADUBBA · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · MAS'ALOLIN JAHILIYYA

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah