Mumini kakkarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah sama da mumini rarrauna, akwai alka…

Musulunci > Ha > Hadith > Abubuwa masu tausasa zukata da waazozi > Mumini kakkarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah sama da mumini rarrauna, akwai alka…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Mumini kakkarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah…

Bayanin hadisin: Mumini kakkarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa mumini gaba dayansa alheri ne , sai dai mumini kakkarfa a imaninsa da kudirin niyyarsa da dukiyarsa da wasunsu daga fuskokin karfi shi ne mafi alheri kuma mafi soyuwa ga Allah - Mai girma da daukaka - daga mumini rarrauna. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa mumini wasicci da yin riko da sabubba a cikin abinda zai anfane shi na al'amuran duniya da lahira, tare da dogaro ga Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka -, da neman taimakonSa, da dogaro gareShi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga gajiyawa da kasala da nauyayawa game da aikata abinda zai yi amfani a duniya da lahira. Idan mumini ya yi kokari a aiki, ya yi riko da sabubba, yana mai neman taimakon Allah, da neman alheri daga Allah, to babu komai akansa sai ya fawwala al'amarinsa gaba dayansa ga Allah, kuma ya sani cewa zabin Allah - Mai girma da daukaka - shi ne alheri. Idan wata musiba ta same shi bayan hakan , to kada ya ce: "Da a ce, ni na aikata da kaza da kaza ya kasance"; "Domin cewa (Da a ce) tana bude aikin Shaidan" A bujirewa kaddara, da dana sani akan abinda ya wuce, sai dai ya ce yana mai mika wuya kuma yana mai yarda: "Kaddarar Allah, abinda Ya so zai aikata", abinda ya afku , kawai shi da hukuncin abinda Allah ya so ne, domin cewa Shi mai aikata abinda Ya yi nufi ne, kuma babu mai juyar da hukuncinSa, kuma babu mai bibiyar HukuncinSa.

Koyarwar hadisin: Mumini kakkarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah…

Rukunan : ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · ILIMIN AƘIDA · AYYUKAN ZUKATA · FALALOLI DA LADUBBA · Imani da Hukuncin Allah da Ƙaddara · MAS'ALOLIN HUKUNCIN ALLAH NA ƘADDARA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah