Allah Ya buga wani misali hanya ce madaidaiciya

Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Allah Ya buga wani misali hanya ce madaidaiciya

Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Allah Ya buga wani misali hanya ce madaidaiciya

عَنْ النَّوَّاسِ بْنِ سَمْعَانَ الْأَنْصَارِيِّ رضي الله عنه عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «ضَرَبَ اللهُ مَثَلًا صِرَاطًا مُسْتَقِيمًا، وَعَلَى جَنْبَتَيْ الصِّرَاطِ سُورَانِ، فِيهِمَا أَبْوَابٌ مُفَتَّحَةٌ، وَعَلَى الْأَبْوَابِ سُتُورٌ مُرْخَاةٌ، وَعَلَى بَابِ الصِّرَاطِ دَاعٍ يَقُولُ: أَيُّهَا النَّاسُ، ادْخُلُوا الصِّرَاطَ جَمِيعًا، وَلَا تَتَعَرَّجُوا، وَدَاعٍ يَدْعُو مِنْ فَوْقِ الصِّرَاطِ، فَإِذَا أَرَادَ يَفْتَحُ شَيْئًا مِنْ تِلْكَ الْأَبْوَابِ، قَالَ: وَيْحَكَ لَا تَفْتَحْهُ، فَإِنَّكَ إِنْ تَفْتَحْهُ تَلِجْهُ، وَالصِّرَاطُ الْإِسْلَامُ، وَالسُّورَانِ: حُدُودُ اللهِ، وَالْأَبْوَابُ الْمُفَتَّحَةُ: مَحَارِمُ اللهِ، وَذَلِكَ الدَّاعِي عَلَى رَأْسِ الصِّرَاطِ: كِتَابُ اللهِ، وَالدَّاعِي مِنِ فَوْقَ الصِّرَاطِ: وَاعِظُ اللهِ فِي قَلْبِ كُلِّ مُسْلِمٍ».

Bayanin hadisin: Allah Ya buga wani misali hanya ce madaidaiciya

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa; Allah Ya buga wani misali ga Musulunci da hanya madaidaiciya mikakkiya babu karkata a cikinta, agefan wannan hanyar akwai ganuwowi biyu, to bangwaye da suke kewaye da ita ta fuskarsa su ne iyakokin Allah, wasu budaddun kofofi suna shiga wadannan ganuwowi biyun su ne Abubuwan da Allah Ya haramta, akan wadannan kofofin akwai labulayen da basa bayyanar da wanda yake cikinsu ga mai wucewa akan hanyar, afarkon hanyar akwai wani mai kira yake fuskantar da mutane kuma yake shiryar da su yana ce musu: Ku tafi akansa ba tare da kun karkace zuwa wani bangaren ba, wannan mai kiran duk lokacin da mai tafiya akan tafarkin ya yi niyyar ya bude wani gwargwado mai sauki daga labulayen kofofin sai ya tsawatar masa ya ce da shi: Kaicanka kada ka bude shi! domin cewa kai idan ka bude shi zaka shigeshi kuma ba zaka sami damar kare kanka ba daga shiga, wannan mai kiran shi ne mai wa'azin Allah a cikin zuciyar kowane Musulmi.

Koyarwar hadisin: Allah Ya buga wani misali hanya ce madaidaiciya

Rukunan : FALALOLI · ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · FALALOLIN ALƘUR'ANI · AYYUKAN ZUKATA · ZARGIN SON ZUCIYA DA SHA'AWE-SHA'AWE · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah