Wanda ya manta alhali yana azumi, sai ya ci ko ya sha, to ya cike aziminsa, kaɗai Allah ne…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Wanda ya manta alhali yana azumi, sai ya ci ko ya sha, to ya cike aziminsa, kaɗai Allah ne…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Wanda ya manta alhali yana azumi, sai ya ci ko ya sha,…
Bayanin hadisin: Wanda ya manta alhali yana azumi, sai ya ci ko ya sha,…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya ci ko ya sha akan mantuwa alhali shi yana cikin azimin farilla ko nafila to ya cika aziminsa kada ya karya; domin cewa shi bai yi nufin karyawa ba, kawai shi wani arziƙi ne Allah Ya koro masa kuma Ya ciyar da shi Ya shayar da shi.
Koyarwar hadisin: Wanda ya manta alhali yana azumi, sai ya ci ko ya sha,…
- Ingancin azimin wanda ya ci ko ya sha akan mantuwa.
- Babu zunubi akan wanda ya ci ko ya sha akan mantuwa; domin cewa shi bada zaɓinsa ba ne.
- Sauƙin Allah ga bayinSa da sauƙaƙa musu da ɗauke wahala da ƙunci daga gare su.
- Mai azimi ba ya karya aziminsa da wani abu daga abubuwa masu karya azimi sai idan sharuɗɗa uku sun cika: Na farko: Ya zama masani, idan ya kasance jahili bai karya azimi ba. Na biyu: Ya zama yana mai tinawa, idan ya kasance yana mai mantuwa, to aziminsa ingantacce ne kuma babu ramuwa akansa. Na uku: Ya zama yana mai zaɓi ba abin tilastawa ba shi ne ya ci abinda yake karya azimi da zaɓinsa.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· AZUMI
· FIƘHU DA USULU
· ABUBUBWA MASU ƁATA AZUMI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا إله إلا الله
Babu abin bautawa sai Allah