Mun yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mubaya'a a kan ji …

Musulunci > Ha > Hadith > Daawa da hisba > Mun yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mubaya'a a kan ji …

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Mun yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabb…

عن عُبَادَةَ بن الصَّامتِ رضي الله عنه قال: بَايَعْنَا رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم على السَّمْعِ وَالطَّاعَةِ فِي الْعُسْرِ وَالْيُسْرِ، وَالْمَنْشَطِ وَالْمَكْرَهِ، وعلى أَثَرَةٍ علينا، وعلى أَلَّا نُنَازِعَ الْأَمْرَ أهلَه، وعلى أَنْ نَقُولَ بِالْحَقِّ أينما كُنَّا، لا نَخَافُ في الله لَوْمَةَ لَائِمٍ.

Bayanin hadisin: Mun yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabb…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya riƙi alƙawari daga sahabbansa wajen jagorantuwa (biyayya) ga majiɓinta al'amura da shugabanni a halin sauƙi da wahala, da halin wadata da talauci, kuma duk ɗaya ne umarninsu ya kasance daga abin da rai yake so ne ko yake ƙi, kai ko da shugabanni sun yi babakere da dukiyar jama'a ko muƙamai ko wanin hakan a kan talakawa; to, dole ne a ji [maganarsu] a yi biyayya bisa sanannun abubuwa, kada a yi musu tawaye, domin fitina da ɓarna wajen yaƙarsu ita ce mafi girma, kuma mafi tsanani daga ɓarnar da za ta faru saboda zaluncinsu, yana daga abin da suka yi alkawari a kansa cewa za su faɗi gaskiya a kowanne wuri suna masu yi wa Allah ikhlasi cikin haka, ba sa jin tsoron wanda zai zargesu.

Koyarwar hadisin: Mun yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabb…

Rukunan : SIYASA A SHARI'ANCE · YI WA SHUGABA TAWAYE · DA'AWA DA HISBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
سبحان الله وبحمده Tsarkin Allah da godiyarSa

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah