Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya …

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya …

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza…

عن أبي سعيد الخُدْريِّ رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «‌مَنْ ‌رَأَى ‌مِنْكُمْ ‌مُنْكَرًا فَلْيُغَيِّرْهُ بِيَدِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِلِسَانِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِقَلْبِهِ، وَذَلِكَ أَضْعَفُ الْإِيمَانِ».

Bayanin hadisin: Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin umarni da canza abin ki - wanda shi ne dukkanin abinda Allah da ManzonSa suka hana - gwargwadon iko, Idan ya ga wani abin ki to yana wajaba akansa ya canja shi da hannu idan yana da iko, Idan ya gajiya akan hakan, to ya canja shi da harshensa, ta hanyar hana mai aikatawar, kuma ya bayyana masa cutar hakan, ya kuma shiryar da shi zuwa alheri maimakon wannan sharrin, Idan ya gajiya daga wannan matakin, to ya canja shi da zuciyarsa shi ne ya ki wannan mummunan aikin, kuma ya yi niyyar cewa shi da yana da iko akan canja shi to da ya aikata, canzawa da zuciya shi ne mafi raunin matakan imani a canja abin ki.

Koyarwar hadisin: Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DAGA MUMMUNA · HUKUNCIN UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DAGA MUMMUNA · Principles of Enjoining Good and Forbidding Evil · DA'AWA DA HISBA · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · ƘARUWAR IMANI DA RAGUWARSA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah