Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi soyuwa a wurin Allah sama da waɗannan …

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi soyuwa a wurin Allah sama da waɗannan …

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya ruwaito shi, da Abu Dawud, kuma lafazin nasa ne

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi soy…

عن ابن عباس رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «ما مِنْ أيَّامٍ العمَلُ الصَّالِحُ فيها أحبُّ إلى اللهِ مِن هذه الأيام» يعني أيامَ العشر، قالوا: يا رسُولَ الله، ولا الجهادُ في سبيلِ الله؟ قال: «ولا الجهادُ في سبيلِ الله، إلا رجلٌ خَرَجَ بنفسِه ومالِه فلم يَرْجِعْ من ذلك بشيءٍ».

Bayanin hadisin: Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi soy…

Annabi tsira da amincin Allah su tabba a gare shi, yana bayyana ayyuka na ƙwarai a goman farko na watan and Zul Hijja (Watan babbar Sallah) ya fi a kan sauran kwanakin shekara.

Sahabbai Allah ya yarda da su, suka tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da Jihadi a kwanakin da ba waɗannan goman ba, shin shi ne ya fi ko kuwa ayyuka na ƙwarai a waɗannan kwanakin? saboda abin da suka sani na Jihadi yana cikin mafificin ayyuka.

Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya amsa da cewa kyawawan ayyuka a waɗannan kwanakin sun fi Jihadi a wasu kwanakin, sai dai mutumin da ya fita yana mai Jihadi da kutsawa hatsari da ransa da dukiyarsa; Don ɗaukaka addinin Allah sai ya rasa dukiyar ta sa kuma ran shi ya fita domin ɗaukaka addinin Allah. To wannan shi ne ya fi a kan aiki na ƙwarai a cikin waɗannan kwanaki masu falala.

Koyarwar hadisin: Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi soy…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · HAJJI DA UMRA · JIHADI · FIƘHU DA USULU · GOMAN ZUL-HIJJA · FALALAR JIHADI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
اللهم صل على محمد Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah