Waye a cikinku yabar abinda ya saba ya bayarwa a gidansa, da dukiyarsa na Al-khairi to yan…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Waye a cikinku yabar abinda ya saba ya bayarwa a gidansa, da dukiyarsa na Al-khairi to yan…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Waye a cikinku yabar abinda ya saba ya bayarwa a gidans…

عن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم بَعَث إلى بني لَحْيَان، فقال: «لَيَنْبَعِث مِن كُلِّ رَجُلَين أَحَدُهُما، والأجرُ بَينَهُمَا».
وفي رواية: «لَيَخْرُجَ مِنْ كُلِّ رَجُلَين رَجُل» ثم قال للقاعد: «أَيُّكُم خَلَفَ الخَارِجَ في أهْلِه وماله بخَير كان له مِثل نِصَفِ أَجْر الخَارجِ».

Bayanin hadisin: Waye a cikinku yabar abinda ya saba ya bayarwa a gidans…

Ya zo a cikin Hadisin Abu Sa'id Al-Khudri -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah SAW yai nufin aika Rundunar Yaki zuwa Bani Lihyan, kuma su ne mafi Shaharar Kabilun Huzail, Kuma Malamai sun hadu kan cewa Bani Lihyan sun Kasance a cikin wancan lokaci Kafirai ne, sai ya aika musu da Tawaga da zasu yake su (Sai ya ce) da waccan runduna (Sai Mutum daya daga kowane mutane biyu ya futa) yana nufin daga kowace Kabila rabin Adadinta, (Kuma ladan) ai baki dayan abun da aka samu na Mayaki da wanda bai je ba yana da Alkairi (a tsakanin su) saboda shi ne Ma'anar fadinsa a cikin Hadisin da yake kafinsa "Kuma waye a cikin ya baro Sallama a gidansa da kuma dukiyarsa da Alkairi? to yana da lada kwatankwacin rabin Ladan wanda ya futa" Ma'ana cewa Annabi SAW ya Umarce su da su futar da daya daga cikin su, wani dayan kuma su bar daya ya maye gurbin Mayaki a gidansa, sai ya zamnato yana da rabin ladansa; Saboda rabin ladan na biyun na Mayaki ne

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · JIHADI · FIƘHU DA USULU · FALALAR JIHADI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah