Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > Ku dinga maimaita wannan Alƙur’anin, ina rantse muku da wanda ran Muhammad yake a hannunSa…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «تَعَاهَدُوا هَذَا الْقُرْآنَ، فَوَالَّذِي نَفْسُ مُحَمَّدٍ بِيَدِهِ لَهُوَ أَشَدُّ تَفَلُّتًا مِنَ الْإِبِلِ فِي عُقُلِهَا».
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi umarnin yawan maimaita Alƙur’ani da dagewa a kan karanta shi; domin kada a manta bayan an haddace shi a zuciya, [Annabi] tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kuma ƙarfafi hakan da rantsuwa a kan Alƙur’ani ya fi saurin ɓacewa da tafiya daga zuciya a kan raƙumi da aka ɗaure, ga shi a ɗaure da igiya a ƙwauri, idan mutum yana yawan bibiyarsa sai ya riƙeshi, idan kuma ya sakeshi sai ya tafi ya ɓace.
Rukunan : ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA · FALALOLI NA ALƘUR'ANI · FALALAR KULAWA DA ALƘUR'ANI