’’Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amuransa alheri ne, kuma hakan ba ya kas…
Musulunci > Ha > Hadith > Abubuwa masu tausasa zukata da waazozi > ’’Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amuransa alheri ne, kuma hakan ba ya kas…
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: ’’Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amura…
Bayanin hadisin: ’’Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amura…
(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana mamaki daga sha'anin mumini da halayensa ta ɓangaren kyautatawa; hakan domin halayensa dukkansu alheri ne, kuma hakan ba ya kasancewa ga wani sai ga mumini; Idan farin ciki ya same shi sai ya godewa Allah; sai ya samu lada saboda godiyarsa. Idan kuma cuta ta same shi sai ya yi haƙuri ya nemi lada a wurin Allah, sai ya samu lada saboda haƙuri, shi a kowanne hali yana cikin lada.
Koyarwar hadisin: ’’Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amura…
- Falalar godiya akan farin ciki da kuma haƙuri akan cuta, wanda ya aikata hakan alherin duniya da na lahira za su same shi, wanda bai godewa ni'ima ba, kuma bai yi haƙuri akan musiba ba, to lada ya wuce shi, kuma zai samu zunubi.
- Falalar imani, kuma cewa lada a kowanne hali ba ya kasancewa sai ga ma'abota imani.
- Godiya a lokacin farin ciki, da haƙuri akan cuta suna daga ɗabi'un mumini.
- Imani da hukuncin Allah da kuma ƙaddararSa yana sanya mumini a cikin cikakkiyar yarda a kowanne halinsa, saɓanin wanin mumini wanda yake kasancewa a cikin fushi, idan ya sami Ni’ima daga Allah madaukakin sarki sai ya shagalta da ita daga biyayya ga Allah, amadadin haka ma sai ya juyar da ita a saɓonSa.
Rukunan :
ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI
· TSARKAKE ZUKATA
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا إله إلا الله
Babu abin bautawa sai Allah