Ya Ubangiji ina roƙonKa shiriya da tsoron Allah, da kamewa, da wadata
Musulunci > Ha > Hadith > Fihun adduoi da zikirai > Ya Ubangiji ina roƙonKa shiriya da tsoron Allah, da kamewa, da wadata
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Ya Ubangiji ina roƙonKa shiriya da tsoron Allah, da kam…
Bayanin hadisin: Ya Ubangiji ina roƙonKa shiriya da tsoron Allah, da kam…
Ya kasance daga addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Ya Allah ni ina roƙonKa shiriya» hanya madaidaiciya na sanin gaskiya da aiki da ita.
«Da tsoron Allah», ruko da umarni da nisantar hane-hane. «Da kamewa» kamewa daga abinda ba ya halatta kuma ba shi da kyau na magana ne ko aiki.
«Da wadatuwa» daga halitta, inda ba zai yi buƙatuwa ba zuwa ga wani inba Uabngijinsa - Mai girma da ɗaukaka ba -.
Koyarwar hadisin: Ya Ubangiji ina roƙonKa shiriya da tsoron Allah, da kam…
- Ɗaukakar waɗannan ɗabi'un: Shiriya da tsoron Allah da kamewa da wadata, da kwaɗaitarwa akan ɗabi'antuwa da su.
- Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya mallakawa kansa wani amfani ko cutarwa, wanda yake mallakar hakan Shi ne Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Wanda yake mallakar amfani da cutarwa da shiryar da halitta Shi ne Allah Shi kaɗai, ba wani mala'ika makusanci ba kuma ba wani Annabi abin aikowa ko waninsu ba.
Rukunan :
FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI
· ADDU'O'I DA AKA RUWAITO
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله
Subhanallah - Tsarkin Allah