Idan ka kasance kamar yadda ka faɗa, to, kamar kana cusa musu toka mai zafi ne a bakin su,…

Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli > Idan ka kasance kamar yadda ka faɗa, to, kamar kana cusa musu toka mai zafi ne a bakin su,…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Idan ka kasance kamar yadda ka faɗa, to, kamar kana cus…

Bayanin hadisin: Idan ka kasance kamar yadda ka faɗa, to, kamar kana cus…

Wani mutum ya kai kuka wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi yana da makusanta da 'yan zumunci yana yi musu kyakkyawar mu'amala su kuma suna yi masa kishiyar haka; sai ya sadar da (zumuncin) su ya zo musu alhali su kuma suna yanke masa (zumunci), yana kyautata musu da yin aikin alheri da cika alƙawari su kuma suna munana masa da zalinci da wauta, yana yi musu haƙuri yana yi musu afuwa, su kuma suna yi masa wauta da mummunar magana da mummunan aiki, shin zai ci gaba da sadar musu (da zumunci) tare da abinda aka anbata?

Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: Idan abinda ka faɗa haka yake to lallai cewa kai kana kunyatasu kuma kana wulaƙantasu akan kansu, kamar cewa kai kana ciyar da su toka ce mai zafi; dan yawan kyautatawarka da kuma mummunan aikinsu daga garesu, kuma wani mai taimakonka a kansu daga Allah, kuma mai tunkuɗe maka cutarsu akan abinda ka anbata na kyautatawarka garesu ba zai gushe tare da kai ba, su kuma su ci gaba akan munanawarsu gareka.

Koyarwar hadisin: Idan ka kasance kamar yadda ka faɗa, to, kamar kana cus…

Rukunan : FALALOLI · FALALOLIN SA DA ZUMUNCI · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
اللهم صل على محمد Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah