Aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma abinda ya sosu a cikin ƙirji, kuma ka…

Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma abinda ya sosu a cikin ƙirji, kuma ka…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma ab…

عَنِ النَّوَّاسِ بْنِ سِمْعَانَ الْأَنْصَارِيِّ رضي الله عنه قَالَ: سَأَلْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الْبِرِّ وَالْإِثْمِ، فَقَالَ: «الْبِرُّ حُسْنُ الْخُلُقِ، وَالْإِثْمُ مَا حَاكَ فِي صَدْرِكَ، وَكَرِهْتَ أَنْ يَطَّلِعَ عَلَيْهِ النَّاسُ».

Bayanin hadisin: Aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma ab…

An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da aikin alheri da zunubi, sai ya ce:

Mafi girman ɗabi'un aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a tare da Allah da tsoron Allah, da kuma halitta, tare da halitta da jure wa cuta, da ƙarancin fushi, da shinfiɗa fuska, da daddaɗan zance, da sadarwa da ɗa'a da tausayi da kuɓutarwa da kyakkyawar mu'amala da abokantaka.

Amma zunubi abinda ya motsu a cikin zuciya na abubuwa masu rikitarwa kuma ya yi kai kawo ba tare da ƙirji ya buɗe gare shi ba, kuma kokwanto ya faru daga gare shi, da tsoron kasancewarsa zunubi, baka so ka bayyanar da shi ba, dan kasancewarsa mummuna ga idanuwa da mutanen kirki da cikakkunsu, hakan domin cewa rai da ɗabi'arta ƙarƙashin tsinkayen mutane akan alherinta, idan ka ƙi tsinkaye akan sashin ayyukanta to shi zunubi ne babu alheri a cikinsa.

Koyarwar hadisin: Aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma ab…

Rukunan : FIƘHUN HALAYE · ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · HALAYE NAGARI · AYYUKAN ZUKATA · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah