Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Dukkan ayyuka (ba sa yiwuwa) sai da niyyoyi, kaɗai kowane mutum (ana ba shi ladan) abin da…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن عمر بن الخطاب رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إِنَّمَا الْأَعْمَالُ بِالنِّيَّةِ، وَإِنَّمَا لِامْرِئٍ مَا نَوَى، فَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُهُ إِلَى اللهِ وَرَسُولِهِ، فَهِجْرَتُهُ إِلَى اللهِ وَرَسُولِهِ، وَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُهُ لِدُنْيَا يُصِيبُهَا أَوِ امْرَأَةٍ يَتَزَوَّجُهَا، فَهِجْرَتُهُ إِلَى مَا هَاجَرَ إِلَيْهِ».
وفي لفظ للبخاري: «إِنَّمَا الْأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ، وَإِنَّمَا لِكُلِّ امْرِئٍ مَا نَوَى».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa dukkanin ayyuka ababen izina ne da niyya, wannan hukuncin mai gamewa ne a cikin dukkanin ayyuka na ibadu da mu'amaloli, wanda ya yi nufin wani abin amfani da aikinsa ba zai samu komai ba sai wannan abin amfanin, kuma babu sakamako gareshi, wanda yayi nufin neman kusanci da aikinsa zuwa ga Allah - madaukakin sarki zai samu sakamako da lada daga aikinsa ko da aikin ya kasance na al'ada ne, kamar ci da sha.
Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya buga misali don bayanin tasirin niyya a ayyuka tare da daidaituwarsu a sura ta zahiri, sai ya bayyana cewa wanda ya yi nufin neman yardar Ubangigjinsa da hijirarsa, to, hijirarsa hijira ce ta shari'a abar karɓa za a yi masa sakayya a kanta don gaskiyar niyyarsa, wanda ya yi nufin wani abin amfani na duniya na dukiya, ko kasuwanci, ko mata da hijirarsa ba zai samu komai daga hijirarsa ba sai wancan abin amfanin da ya yi niyyarsu, kuma ba zai samu lada da sakamako ba.
Rukunan : ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · AYYUKAN ZUKATA · FALALOLI DA LADUBBA